Ba na son yin yaki da Iran – Trump

Hassan Rouhani and Donald Trump Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sa-in-sa na karuwa tsakanin Shugaba Hassan Rouhani da Shugaba Donald Trump

Manyan jami'an gwamnatin Amurka sun ce Shugaba Trump ba ya son yin yaki da Iran a lokacin da kasashen biyu ke ci gaba da 'yar tankiya a tsakaninsu.

A wata ganawa da suka yi ranar Laraba, shugaban ya shaida wa mataimakansa cewa ba ya son matsin lambar da Amurka ke yi ya rikide zuwa rikici.

Amurka ta aika jiragen ruwan yaki da na sama zuwa iyakar Tekun Fasha, ta kuma janye jami'an diflomasiyyarta daga Iraki a baya-bayan nan.

Jami'ai sun ambato cewa Iran tana yin barazana kan hakan.

An zargi Tehran da zuba makamai masu linzami a jirgin ruwa a Tekun Fasha, kuma rahotanni sun ce masu binciken Amurka sun yi amannar cewa kasar ta lalata tankokin dakon man fetur hudu a gabar tekun kasar Hadaddiyar Daular Larabawa - zargin da Iran ta musanta.

Amma da manema labarai suka tambaye shi a ranar Alhamis kan ko Amurka za ta yi yaki da Iran, sai Mista Trump ya amsa da cewa: "Ba na fatan haka."

Me ya faru a baya-bayan nan?

Jaridar New York Times ta ruwaito cewa sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yana tuntubar kawayen kasar da ke Turai da sauran wurare kan taimakonsu wajen yayyafawa lamarin ruwa.

Wata sanarwa ta ma'aikatar harkokin kasashen waje ta Amurka ta fitar ta ce Mr Pompeo ya yi magana da Sarkin Oman Sultan Qaboos Bin Said Al Said, a ranar Laraba, kan "barazanar Iran ga kasashen da ke yankin Tekun Fasha.

Sarkin ya dade yana shiga tsakani kan lamarin Iran da kasashen yamma, da suka hada da tattaunawa kan yarjejeniyar nukiliya a karkashin mulkin Shugaba Barack Obama.

Kiran ya biyo bayan bulaguron Mista Pompeo zuwa Rasha, inda ya ce kasarsa ba ta neman rikici, amma ta kara da cewa Amurka "za ta mayar da martanin da ya dace" idan har aka taba mutuncinta.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Zaman tankiya na karuwa a 'yan kwanakin nan tsakanin Iran da Amurka

A hannu guda, kuma shi ma jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya ce ba za a yi rikici ba.

"Ba ma neman yaki, su ma kuma haka," kamar yadda ya fada a wani jawabi da ya yi a kafar yada labaran kasar.

Rahotanni sun ce jiragen ruwa na yaki na Amurka sun wuce ta gabar Tekun Hormuz salin alin a ranar Alhamis.

Me ke faruwa a yankin Tekun Fasha?

A cikin kwanaki kalilan, Amurka ta girke babban jirgin ruwa mai daukar jiragen yaki mai suna USS Abraham Lincoln a yankin, kuma rahotanni sun ce tana ta tsara yadda za ta tura dakaru 120,000 yankin Gabas Ta Tsakiya.

An bai wa jami'an diflomasiyya umarnin barin Iraki, kuma sojojin Amurka sun kara barazana a yankin kan bayanan sirri da suka samu na zargin cewa dakarun da Iran ke goyon baya na girke a wajen - abun da ya ci karo da bayanan wani Janar din sojan Birtaniya, wanda ya ce babu karuwar barazana.

Sojojin Jamus da na Netherlands sun ce sun dakatar da atisayen soji da suke yi a kasar.

Rikicin na baya-bayan nan dai ya zo ne bayan da Iran ta yi watsi da alkawarin da ta yi na yarjejeniyar kasa da kasa ta 2015 kan nukiliya, inda ta yi barazanar ci gaba da samar da makamashinta na uranium.

Manufar yarjejeniyar ita ce janye takunkuman da aka kakabawa Iran don kawo karshen shirin nukiliyarta, amma Amurka ta janye daga yarjejeniyar a bara ta kuma kakaba sabbin takunkumai.

Labarai masu alaka