Hatsarin jirgin sama a Dubai ya yi sanadin mutuwar mutum hudu

View of Dubai airport with city in background Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mutum hudu sun rasa rayukansu a sandin wani hatsarin jirgin sama da ya fado kimanin kilomita uku yamma da babban filin jigin saman Dubai.

Hukumomin Hadaddiyar Daular Larabawa sun ce uku daga cikin mamatan 'yan Birtaniya ne, daya kuma dan Afirka ta Kudu ne.

Dukkansu na cikin wani jirgin sama ne samfurin DA42.

Jirgin mai iya daukar mutum hudu mallakin kamfanin Flight Calibration Services da ke filin jirgin sama na Shoreham a yankin West Sussex na Ingila.

An fara gudanar da bincike kan dalilin wannan hatsarin.

Rahotanni daga kafafen watsa labarai na Dubai na cewa jirgin ya fado ne da misalin karfe 7:30, inda direban jirgin da mataimakinsa da kuma fasinjoji biyu dake cikin jirgin suka gamu da ajalinsu.

An rufe filin jirgin sama na Dubai har tsawon minti 45 bayan hatsarin, inda aka karkatar da akalar wasu daga jiragen sama da ke neman izinin sauka da fasinjojinsu.

Labarai masu alaka