Sheikh Nuhu Sharubutu
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda na ji a lokacin da aka ce zan mutu - Sheikh Sharubutu

Latsa alamar hoton da ke sama domin kallon hirar da Abdulbaki Jari ya yi da Sheik Sharubutu

Babban limamin kasar Ghana mai shekaru 100, Sheikh Nuhu Sharubutu ya bayyana cewa faston da ya ce zai mutu ya zo ya roke shi gafara.

Sheik Sharubutu ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da sashen Hausa na BBC.

A kwanakin baya ne dai wani fasto mai suna Owusu Bempah ya ce a shekarar 2019 Sheik Sharubutu zai mutu wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce.

Da aka tambayayi Malamin ko ya ya ji game da maganar wani faston kan cewa a shekarar 2019 zai mutu? Sai ya ce "Ai abu ne na Allah." "Shugaban kasa ma da kansa ya yi masa fada. 'Yan uwansa ma sun yi masa fada.''

Sheikh Sharubutu ya bayyana cewa Faston ya zo har gidansa inda ya nemi afuwa a kan furucin na sa.

Babban limamin ya shaida cewa asalinsa duka daga Najeriya ne. Mahaifinsa daga Kukawa ta kasar Borno.

Mahaifiyarsa kuma daga Rafindadi a cikin garin Katsina.

Cikakkiyar wannan hirar na shafinmu na youtube.

Labarai masu alaka