Godwin Emefiele: Kalubalen da ke gaban Gwamnan Babban Bankin Najeriya

Godwin Emefiele Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Godwin Emefiele

Tun bayan da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake zabar Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya, masu sharhi musamman kan tattalin arziki na ta sharhi kan irin kalubalen da ke gaban gwamnan da kuma yadda zai yi ya shawo kansu.

Tuni dai majalisar dattawa a Najeriyar ta tantance Mista Emefiele kuma ta amince da ya sake koma wa wa'adi na biyu inda zai shafe shekaru biyar yana jan ragamar bankin kamar yadda ya faro a 2014.

BBC ta tuntubi Abubakar Aliyu wanda wani mai sharhi ne kan tattalin arziki a Najeriya inda ya lissafo kalubale akalla biyar da suke gaban Emefiele.

Shawo kan matsalar hauhawar farashin kayayyaki

Duk da cewa a kwanakin baya hukumar bayar da kididdiga ta Najeriya ta bayyana cewa kasar ta fita daga matsi na tattalin arziki, har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da batun hauhauwar farashi musamman na kayayyakin masarufi.

Abubakar Aliyu ya bayyana cewa dole ne babban bankin Najeriya ya tabbatar da cewa bankuna sun bayar da bashi musamman ga kamfanonin da ke sarrafa kayayyaki a farashi mai rahusa domin samar da kayayyaki.

Ya kuma bayyana cewa dole a tabbatar da cewa an rage bai wa gwamnati bashi wanda a halin yanzu abin da ke faruwa kenan kamar yadda mai sharhin ya bayyana.

Masana a Najeriya dai na ganin cewa hauhawar farashi na baya-bayan nan ya samo asali ne tun a shekarar 2015 da farashin danyen man fetur ya fara faduwa a kasuwar duniya sakamakon yawan fitar da shi da ake yi.

Hakan ya yawo yawan kudaden kasashen wajen da Najeriyar take samu ya ja baya sosai.

Sakamakon haka kuma mutane, musamman 'yan kasuwa, da ke shigo da kayayyaki suka fara fuskantar matsala wajen samun kudin musaya.

A duk kuwa lokacin da bukatar dala ta yi yawa, to farashin dalar kan karu ne a hukumance da kuma a kasuwar bayan fage.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Farfado da darajar Naira

A yanzu haka dai, naira ta sha kashi ko kuma a ce ta sha wuya a hannun kudaden kasashen waje musamman dalar Amurka da fam din Ingila.

A shekarun baya da ba su wuce biyar ba, akan yi musayar kudin Najeriya da kuma dalar Amurka kasa da naira 200 kan ko wace dala daya, a halin yanzu kuma abin ya yi nisa inda ake samun musayar kudin kan sama da 360 a kowace dala a kasuwannin bayan fage.

Malam Abubakar ya bayyana cewa ya zama dole ga gwamnan babban bankin ya fito da matakai da za a bi wajen farfado da darajar naira domin ta dawo tana gogayya da sauran kudade.

Kamar yadda tarihi ya nuna, naira ta fi dala daraja a shekarun baya sama da shekaru talatin kenan, wanda daga baya har suka zo suna tafiya kafada da kafada har dalar ta zo ta wuce naira sosai.

Kula da asusun ajiya na kasar waje (Foreign Reserve)

Wannan asusu ne mai matukar amfani musamman ga tattalin arziki.

Ko wace kasa a duniya tana da irin wannan asusu kuma wannan asusu na daya daga cikin abubuwan da ake dubawa domin auna mizanin tattalin arzikin kasa.

Malam Abubakar ya bayyana cewa dole ne Emefiele ya tabbatar da cewa ya gina wannan asusun da kuma inganta shi.

Ya ce inganta shi da kuma yawanshi zai iya sa darajar kudin Najeriya ta farfadowa.

Ya bayyana cewa da wannan asusun ne ake amfani domin biyan bukatar wasu kamfanoni inda ake basu bashi su sawo kayayyaki domin sarrafa su cikin kasa.

Ya bayyana cewa kula da wannan asusu babban aiki ne ga gwamnan babban bankin, ganin cewa danyen man fetur har yanzu bai da wani tasiri a kasuwannin duniya.

Samar da kudade a kasa

Mai sharhi ya bayyana cewa daya daga cikin kalubalen da ke gaban Emefiele shi ne tabbatar da sa ido da kuma fito da tsare-tsare da za a ga cewa kudade na yawo a hannun jama'a.

Ya bayyana cewa ko bankuna ma na kokawa a halin yanzu inda ya ce ba kowane banki mutum zai je yana bukatar kudinsa da yawa a dauka a ba shi ba.

Ya ce aikin babban bankin ne ya ga cewa an samu wadatattun kudade daidai gwargwado ba kuma kudin su yi yawa ba, amma samar da kudaden zai kara kawo sauki ga tattalin arziki.

Ta wace hanya Godwin Emefiele zai dawo da martabarsa?

Jama'a da dama a Najeriya na ta sukar matakin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dauka na kara wa'adin Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin kasar karo na biyu.

'Yan kasar da dama na ganin cewa bai tabuka wani abin a zo a gani ba wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya bayan fadawar kasar cikin matsi da kuma tabarbarewar tattalin arziki a kwanakin baya.

Sai dai mai sharhin wato Abubakar Aliyu ya bayyana cewa abu ne da kamar wuya da har 'yan Najeriya za su gani su ce sun gamsu.

Ya bayyana cewa duka wadannan kalubalen da aka lissafa a sama, ayyukan babban bankin Najeriya ne tun daga hauhawan farashi zuwa farfado da darajar naira da samar da kudade da kula da asusun Najeriya, sai dai kuma duk an samu matsala a wadannan bangarori.

Ya bayyana cewa amma babban abin da yakamata a ce Emefiele ya yi da zai dawo da matartabarsa a idon 'yan Najeriya, shi ne dawo da darajar naira.

Dawo da darajar naira zai kawo sauki kwarai ga jama'a da 'yan kasuwa da ita gwamnatin kanta.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ya bayyana cewa a shekaru biyar da Emefiele ya shafe kan kujerarsa, abin da ya fi bayar da karfi a kai shi ne shirin bayar da bashi ga manoma wato ''Anchor Borrower programme.''

Ya bayyana cewa wannan shiri ne mai kyau amma duk da haka ba a samu abin da ake so ba domin kuwa farsashin kayayyakin abinci har yanzu akwai tsada sosai.

Mai sharhin ya ce abin da yakamata a yanzu, gwamnan babban bankin kasar ya bayar da shawara ga gwamnati domin ganin cewa an sauya fasalin asusun bai daya na gwamnati wato ''Treasury Single Account'' da aka fi sani da TSA.

Kamar yadda ya bayyana, ya ce ba lallai ne a ce duk kudin da gwamnati ta samu ba za a saka a wannan asusun, akwai kudade da za a iya kai wa bankunan masana'antu ko kuma na kasuwanci da za su taimakawa mutane.

Malam Abubakar ya bayyana cewa a baya akwai basussuka da yawa wadanda da yardar Emefiele ne bankunan kasuwanci suka ba gwamnatocin jihohi wanda hakan ya sa a halin yanzu wadannan bankuna ba su da kudaden da za su bayar da bashi ga kananan 'yan kasuwa ko kuma kamfanoni.

Ya ce ya kamata a ce a samo kudi ko da daga asusun ajiya na kasar waje ne (Foreign Reserve) domin mayar wa wadannan bankuna ta yadda bankunan za su ba mutane bashi domin kudade su shiga hannun mutane.

Labarai masu alaka