Tattaunawa da mawakin nan na Ghana mai suna Zeal
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Dalilin da ya sa wakokin Najeriya suka fi na Ghana- Mawakin Ghana

BBC Hausa ta samu tattaunawa da fitaccen mawakin nan na Ghana mai suna Zeal, wanda aka fi sani da Lazy na kungiyar mawaka ta VVIP, wacce a da take VIP.

Asalin sunansa dai Abdulhameed Ibrahim, kuma ya yi fice sosai a yammacin Afirka.

Daya daga cikin wakokinsa Ahomka Womu ta yi fice a kasashen yammacin Afirka musamman Ghana da Najeriya. A cikin tattaunawar, ya shaida wa BBC dalilin da ya sa ya sauya sunansa ''Lazy,'' wato mai kiuya da Hausa zuwa ''Zeal.''

Ya kuma bayyana dalilin da ya sa wasu daga cikin abokansa na kungiyar ta su suka fita daga ciki.

Labarai masu alaka