Mece ce makomar Gareth Bale a Real Madrid?

Gareth Bale Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Dan wasan kasar Wales din ya shafe shekara shida a Santiago Bernabéu

Kakar bana ba ta kare wa Gareth Bale da dadi ba a Real Madrid yayin da ya zauna a benci a wasan karshe na gasar La Ligar bana, wanda Real Betis ta doke Madrid da ci 2-0.

Bayan sun kare a mataki na uku maki 19 a gasar zakarun Barcelona kuma aka karya kwarinsu na kofin Zakarun Turai uku da suka lashe a jere, kocin kungiyar Zinedine Zidane na kokarin gina sabuwar tawaga.

Bale bai ji dadin yadda aka kammala wasan karshen ba yana benci.

Ya shafe shekara shida a kasar Spain, inda ya lashe kofuna 13 kuma ya kamo dan wasa Phil Neal a matsayin dan Birtaniya da ya fi kowa lashe kofuna.

Dan wasan ya cika alkawarin da ya dauka lokacin da ya je Madrid cewa "zai zama dan wasan Birtaniya da ya fi kowa taka rawa a wajen Birtaniya".

Zabin Zidane na ya raba gari da dan wasan kasar Wales din yana cike da rudani ganin irin girman yarjejeniyarsa.

Bale yana da fam milyan 55 a cikin kwantiraginsa, inda zai kare a 2022. Idan aka yi dalla-dalla, baki dayan albashin da kungiyar Huddersfield Town ta firimiyar Ingila ta biya a kakar 2017-2018 fam miliyan £62.6 ne.

Saboda indai Bale yana son barin kulob din to sai fa Real Madrid ta tallafawa kulob din da yake son sayan sa wajen rage darajarsa.

Ko dai a rage kudin sayensa, ko a rage masa albashi koi kuma bayar da aronsa.

Babu wani mai sauki a cikin wadannan zabubbuka a lokacin da Zidane ke son ya yi wa kungiyar garambawul, wanda zai hada da zuwan Hazard daga Chelsea kan kudi kusan fam miliyann 100.

Wa ke son sa?

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Manchester United sun dade suna zawarcin dan wasan. Amma dan wasa mai tsada da suka saya na baya-bayan nan shi ne Alexis Sanchez, wanda bai taka wata rawar a-zo-a-gani ba.

Tabbas Ole Gunnar Solskjaer yana cikin wani yanayi tsakaninsa da Sanchez kamar na da Zidane da Bale.

Abu ne mawuyaci United ta hada Bale da Sanchez 'yan shekara 29 kowannensu a filin kungiya a Old Trafford ganin yadda Solskjaer ke kokarin tattara matasan 'yan wasa domin neman cin kofuna a kaka mai zuwa.

Saboda haka ba za a iya tabbatarwa ba ko za a ga Bale a Old Trafford a yanzu.

Akwai kuma damuwar cewa ko Bale zai yadda ya je kungiyar da ba za ta buga gasar Zakarun Turai ba.

Labarai masu alaka