Mutum biyu sun mutu a hargitsin Kaduna

Rikici a jihar Kaduna Hakkin mallakar hoto AWWAL TASLEEM

Rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta yi karin haske game da wani al'amari da ya faru wanda ya haifar da mutuwar akalla mutum biyu da safiyar ranar Litinin a garin Kaduna.

Bayanai dai sun nuna cewa wani mutum ne ya nemi daukin al'umma bayan da ya yi ikirarin cewa wasu masu garkuwa da mutane na biye da shi a cikin mota.

Hakan ya jawo wasu mutane su far wa mutanen da mutumin ya nuna a matsayin masu satar mutanen, tare da hallaka daya daga cikinsu.

Sai dai mai magana da rundunar 'yan sandan jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo, ya bayyana cewa mutumin da ya yi kwaroroton masu satar mutane na binsa ya yi wa mutanen kazafi ne don tsira daga jami'an tsaro.

DSP Sabo ya ce jami'an 'yan Sandan jihar Legas sun zo jihar Kaduna ne don gudanar da bincike kan mutumin mai suna Alhaji Musa, mazaunin Kaduna.

Shi dai Alhaji Musa ya taba shiga tarkon 'yan sandan jihar Legas bisa wani laifi da ya aikata a can, kuma wasu abokan kasuwancinsa hudu sun tsaya masa a lokacin da yake tsare a wajen 'yan sandan.

Hakkin mallakar hoto AWWAL TASLEEM

Asali ma su ne suka sa masa hannu a matsayin wadanda za su tsaya masa, kuma rundunar 'yan sandan jihar Legas ta bayar da belinsa bisa sharadin zai dawo ya fuskanci shari'a.

Bayan haka sai Alhaji Musa ya koma Kaduna kuma ya ki koma wa Legas duk da alkawarin da ya dauka da kuma abokan huldarsa hudu da suka samu kansu tsundum cikin shari'arsa.

"Abokan kasuwancin nasa hudu sun yi dukkan mai yiwuwa don jawo hankalinsa ya koma Legas ya fuskanci shari'a amma ya ki," in ji DSP Yakubu Sabo.

Don haka ne, 'yan sandan jihar Legas suka yanke shawarar yin takakkiya har Kaduna domin tasa keyarsa, kuma suka nemi taimakon abokan nasa hudu don yi musu jagora zuwa muhallinsa da ke Kaduna.

Sai dai a lokacin da suka iso jihar Kaduna, 'yan sandan Legas sun fara zarcewa hedkwatar rundunar 'Yan Sandan jihar Kaduna ne domin tabbatar da an sanya masu hannu kan takardunsu don fadada binciken.

Daga nan, su kuma abokan kasuwancin Alhaji Musa sai suka nufi gidansa don ganin ko za su shawo kansa cikin laluma ya kai kansa wurin 'yan sanda.

"Sun same shi a daidai lokacin da ya fito zai kai yaransa makaranta, don haka sai suka bi shi a baya a motarsu," in ji kakakin 'yan sandan.

"Da ya gane su ne, sai ya tsaya a daidai babbar gadar Kawo ya yi yekuwar cewa su masu garkuwa ne da mutane kuma ya yi kira mutane su taimake shi," in ji DSP Sabo.

Nan da nan wasu matasa suka taru suka far wa mutanen har suka kashe daya kuma suka yi wa daya mummunan rauni, yayin da biyu kuma suka sha da kyar.

Jami'an tsaro sun zo wurin ne a daidai lokacin da matasan ke "shirin kona daya daga cikin mutanen."

Hakkin mallakar hoto AWWAL TASLEEM

DSP Sabo ya ce babu bayanin da jami'an tsaron ba su yi wa matasan ba a kan cewa mutanen ba masu garkuwa da mutane ba ne, kamar yadda Alhaji Musan ya yi ikirari, amma sai abin ya ci tura.

Ya ce "sun yi ta yunkurin sai lallai a ba su ragowar mutanen nan uku da aka ceto suma su kashe su."

Da jami'an tsaro suka ki sai matasan suka fara kai wa 'yan sandan hari, wanda kuma hakan ya sa jami'an tsaron yin harbi da bindiga don tarwatsa gungun matasan inda harsashi ya samu daya daga cikin matasan har ya mutu.

A halin yanzu dai Alhaji Musa ya tsere a lokacin da hargitsin ya barke kamar yadda DSP Sabo ya shaida wa BBC, sai dai ya ce suna dukkan mai yiwuwa don ganin an kamo shi ya fuskanci shari'a.

DSP Sabo ya ce rundunar 'yan za ta kama duk wadanda suka dau doka a hannunsu dangane da wanna batu don kuwa wannan dabbanci ne kuma rundunarsa ba za ta amince da haka ba.

A Najeriya dai, musamman a yankin kudanci sau da yawa al'umma kan dauki doka a hannunsu idan aka zargi wani da aikata laifi musamman na sata.

A shekarar 2012 ne aka kashe wasu samari hudu daliban jami'ar Fatakwal ta hanyar kona su da taya bayan da aka yi musu kazafin sata a wani kauye a jihar Ribas, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a fadin duniya kuma aka yi masu lakabi da Aluu 4.

Labarai masu alaka