Ana cin tarar 'matan da suka haihu a gida' a Tanzania

Tanzania Hakkin mallakar hoto Getty Images

Za a fara cin tarar matan da ba su haihu a asibiti ba tsakanin dala tara zuwa dala 22 (kimanin naira 3,200 da kuma 8,000) a yankin arewa maso yammacin kasar Tanzania, kamar yadda jaridar The Citizen ta ruwaito.

Ana tilasta wa mata biyan tarar lokacin da suka je asibiti don karbar allurar rigakafi ga 'yayensu a garin Kibondo wanda ke yankin Kigoma, in ji rahoton.

"Matanmu sukan biya tsakanin Tanzanian Shilling 20,000 ($9) zuwa 50,000 ($22) lokacin da suka je neman magani a asibiti bayan sun haihu a gida. Ba za mu yarda da wannan ba," in ji Nicolaus Sabuni, wani mazaunin Kibondo.

Jaridar ta ce babban jami'in lafiyar yankin Innocent Sunamie ya umarce jami'an jinya da su daina cin matan tara ko kuma su fuskanci fushin hukuma.

Karanta wasu karin labarai

Labarai masu alaka