Mun gama da masu satar mutane – Sufeton 'Yan Sandan Najeriya

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Aikin samar da tsaro bai gagari 'yan sanda ba – Sufeton 'Yan Sanda
  • Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon

Babban Sufeton 'Yan sandan Najeriya Mohammed Adamu ya ce jami'an tsaro sun ci galaba a kan masu satar mutane don neman kudin fansa a kasar.

Sai dai ya ce akwai sauran aiki a gaba "don ba wai gaba daya muka gama da su ba. Amma mun ci galaba a kansu sosai-sosai."

Babban sufeton ya ce suna bakin kokarinsu wajen ganin sun kawo karshen matsalar satar mutune a kasar.

Ya bayyana hakan ne lokacin wani taro na shugabannin 'yan sanda da sauran jami'an tsaro da ke yankin Afirka ta yamma (WAPCCO) a makon jiya.

Kazalika ya musanta batun da wasu masu sharhi suke cewa tsaron cikin gidan kasar ya gagari 'yan sanda.

"Sojoji suna aiki da 'yan sanda ne don su taimaka, amma duk inda ka tafi a duniya idan dai maganar tsaro na cikin gida ne 'yan sanda ne ke kan gaba."

Ya ce dukkansu suna yi wa gwamnati ne aiki, "kuma abin da dan Najeriya ke so shi ne zaman lafiya."

"Aiki ba wai ya gagari 'yan sanda ba ne, dole ne mu hada kai da sojoji da jami'an tsaro na DSS da sauransu don tabbatar da tsaro."

Daga nan ya ba da tabbacin cewa "nan ba da jimawa ba Insha Allahu abubuwan za su zo karshe."

A farkon watan Mayu Shugaban Najeriya Buhari ya yi barkwanci da cewa ya ga sufeton 'yan sandan Najeriyar ya rame bayan ya sauka a filin jirgin saman Abuja daga birnin Landan.

A cewar Buhari wannan alama ce ta cewa sufeton yana aiki tukuru game da tsaron kasa.

Har yanzu ana ci gaba da samun rahotannin garkuwa da mutane a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna duk da irin tabbaci da 'yan sandan suka sha bayarwa.

Labarai masu alaka