Abin da ya sa mutane suka yi zanga-zanga a Katsina

An yi zanga-zanga a Batsari Hakkin mallakar hoto @sadiq_mallah

Kura ta lafa a garin Batsari na jihar Katsina, bayan arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga da ke nuna rashin jin dadinsu da tabarbarewar halin tsaro a jihar.

Masu zanga-zangar sun fusata ne da kisan mutane fiye da 13 a wani kauye da ke kusa da garin, kuma daga cikin wadanda aka kashe akwai yara kanana.

Wasu rahotanni sun ce an kuma kai hare-hare a yankunan Dan Musa da Faskari.

Wani mazauni Batsari ya ce 'yan bindiga sun bude wuta ne kan mutanen da suka fita gona yin shuka da safiyar ranar Talata.

Ya ce hatsaniyar da aka samu ta tashi ne bayan da mazauna kauyen da ake kira 'Yar Gamji suka kwaso gawawwakin mutanen suka jibge a kofar gidan mai garin Batsari.

"Dama akwai dubban 'yan gudun hijira a garin, shi ya sanya mutane suka fito zanga-zanga domin nuna bacin ransu kan matsalar tsaro," in ji shi.

Ya kuma ce masu zanga-zangar suna cewa ne a dauki matakin gaggawa domin kawo karshen kashe-kashen rayukan mutane da ake yi kusan a kullum a yankin.

Hare-haren 'yan bindiga da satar mutane don kudin fansa na ci gaba da karuwa a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna duk da yunkurin jami'an tsaro na kawo karshen matsalar da ta addabi yankin arewa maso yammacin kasar.

Mutane da dama ne dai suka rasa rayukansu, yayin da yara da dama suka kasance marayu sakamakon kashe-kashen da ke faruwa a jihohin.

Hakkin mallakar hoto @bash2ruma
Image caption An yi kone-konen tayoyi, masu zanga-zangar sun yi arangama da 'yan sanda

Labarai masu alaka