Dangantakar Bollywood da siyasar India

Jaruman Bollywood da Firaminista Narendra Modi Hakkin mallakar hoto Outlook India

Dangantaka tsakanin masana'antar fina-finan Bollywood da siyasar Indiya ta faro ne daga tushe.

A 1947 Jawaharlal Nehru ya zama fira minista, kuma a lokacin ne kasar ta tsaya kan duga-duganta a matsayin k'asa 'yantacciya, yayin da masana'antar fina-finan Hindi ta taso da karfinta a matsayin d'aya daga cikin bangarorin da sai da su ake damawa a kasar.

Shekarun farko-farko na sinimun Indiya, na da matuk'ar alak'a da gwagwarmayar Mahatma Gandhi da Jawaharlal Nehru game da rashin tarzoma da k'arfafa gwiwar maza da yak'i da shafaffu da mai da had'in kan musulmi, wadannan sak'wanni su ne jigo.

Tabbas a farkon shekarun 1950, masu shirya fina-finai na amfani da shirye-shiryensu wajen fito da matsin rayuwar talakawa da kuma matsalolin zamantakewar da suke jin an yi biris da su.

Duk manyan taurari a zamanin da fina-finan suka yi gagarumin tashe na fadar wani abu game da siyasa a cikin fina-finansu ya Allah Dilip Kumar ne ko Deva Nandh ko Raj Kapoor.

Fina-finai na taka rawa tamkar wani dank'o da ke k'ok'arin had'a kan k'asa, da neman kishin k'asa saboda inda suke shiga na da matuk'ar yawa.

Wani jarumi ko darakta da zai zo wa mutum a rai shi ne Manuch Kumar wanda fina-finansa ke k'unshe da jigon kishin k'asa, kuma suna da gagarumar karbuwa.

Hakkin mallakar hoto India Today

A shekarun 1960 kuma, alak'ar fina-finan Bollywood da siyasar Indiya ta dauki wani sabon salo, inda jarumi kuma mai shirya fina-finai Prithviraj Kapoor, mahaifin Raj Kapoor, kaka ga Rishi Kapoor kuma kakan-kakan Ranvir da Karina Kapoor ya shiga jam'iyyar Congress.

Aboki ne ga Nehru kuma tuni ya nuna alamun fadakarwa da siyasa.

Bayan shekara 20 kuma sai taurarin mashahurin fim din nan Mother India, Nargis da Sunil Dutt, su ma suka shiga jam'iyyar Congress.

Sai dai ba kowanne tauraro ne kan juya da k'afar dama ba.

Hakkin mallakar hoto Latest News

Ga misali, ana kallon shigar Amitabh Bachchan siyasa a matsayin daya daga cikin babbar rashin nasara daga masana'antar fina-finan Bollywood.

Ya tsallaka siyasa don tallafa wa abokinsa Rajiv Gandhi, wanda shi ne Fira minista a shekarar 1984.

Mista Bachchan ya dakatar da shiga fina-finai inda ya tsaya takara daga Alavaav kuma ya lashe zaben da gagarumin rinjaye, amma kuma bai dad'e ba sai aka neme shi aka rasa.

Shi ma kuma siyasar ta fita daga ransa lokacin da aka yi zargin akwai hannunsa a abin kunyar kwanturagin sayen makamai ta Bofor, daga bisani ne ya yanke shawarar barin siyasa kuma ya yi alk'awarin ba zai sake komawa ba.

Hakkin mallakar hoto Quora

Shi ma mashahurin tauraron shekarun 1990 Govinda, ya sha suka kan k'arancin halartarsa da rashin sanin abin da mutanen mazabar ke so.

To ko me ya sa mutane suke zabar jarumai kan mukaman siyasa?

Akasarin jaruman fina-finan Indiya da ke shiga siyasa, sun wuce ganiyarsu, to kuma suna son yin amfani da duk irin daukakar da suke da ita a wajen jama'a don harkokin siyasarsu.

Wannan karon, zak'ak'uran taurari da dama sun tsaya takara sai dai babban sauyin shi ne daga jam'iyyar Congress zuwa jam'iyyar BJP.

Labarai masu alaka