Za a daure duk wanda aka kama yana bara a Uganda

Uganda ta haramta bara a Kampala Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mahukunta a birnin Kampala na Uganda sun haramta yin bara a dukkanin birnin.

Kansiloli a birnin ne suka amince da dokar haramcin musamman yara da tsoffi da ke yawo kan titi suna bara.

Dokar ta shafi daurin watanni shida a gidan yari ga duk wanda ya bayar da abincin sadaka ko kudi ga yaro a kan titunan Kampala.

Sannan za a ci tarar mutum kudi dala $11 wato kimanin naira 4,000 ke nan.

Abu ne dai da aka saba gani yara 'yan kasa da shekara bakwai kan titi suna talla da kuma yin bara a Kampala.

Gwamnati ta ce akwai yara fiye da 15,000 'yan tsakanin shekara bakwai zuwa 17 da ke yawo kan titi suna bara, kuma kullum adadin sai karuwa yake.

Dokar ta kuma haramta fataucin yara daga kauyuka zuwa birni da kama gida dominsu.

An kuma haramta wa manyan mutane sayar da kayayyaki kan titi a birnin.

Labarai masu alaka