An dawo da wani littafin dakin karatu na Donegal bayan shekaru 80

The White Owl Hakkin mallakar hoto Donegal County Council
Image caption An dakatar da cin tarar mutanen da basu mayar da litattafai ba a dukkanin dakunan karatun da ke Ireland a cikin watan Janairun da ya gabata.

An dawo da wani littafi wanda aka ara daga wani dakin karatun da ke Ireland bayan shekara 80 da ya kamata a mayar da shi.

An ari litafin The White Owl, wanda Annie MP Smithson ta rubuta tun a 23 ga watan Yuli na shekarar 1937 daga dakin karatun Donegal da ke yankin Gaeltacht na Gweedore.

An dawo da litaffin zuwa dakin karatu na Gweedore a ranar 17 ga watan Mayu.

An tsinci littafin yayin wani gyaran da aka yi a wani gida da ke garin Falcarragh.

Hakkin mallakar hoto Donegal County Council
Image caption Wani rubutu a cikin litaffin ya nuna cewa an are shi ne tun a watan Yulin shekarar 1937

Wani babban mai kula da dakin karatun Denis McGeady ya ce ya yi mamaki sosai da ya ga an dawo da littafin bayan fiye da shekara 80.

''Mamaki ya turnuke ni a ranar Juma'a da na ga an dawo da littafin bayan shekaru da yawa haka,'' ya ce.

''Ba sabon abu ba ne ba don an dawo da littafi bayan shekara biyu ko uku, amma wannan lamarin dai ba mu saba ganinsa ba.''

'Kar ku ji tsoro'

Ya ce littafin ya zama na musamman.

''Wannan ita ce wallafa ta farko ta littafin The White Owl wanda aka wallafa a 1937, kuma tun a shekarar aka ari littafin kuma da alama lokacin yana sabo kenan''

Hakkin mallakar hoto Donegal County Council
Image caption Dokokin dakin karatun tun 1930 na cewa wadanda suka ari littatafai dole su dawo da su cikin mako 2.

Ya kara da cewa: ''Mun yi bincike a cikin wasu dakunan karatu kuma mun gano cewa babu irin wannan littafin da aka dawo da sosai.''

An bai wa wanda ya ari littafin kwanaki 14 domin ya dawo da shi amma bai kawo shi ba sai bayan shekara 82.

An dakatar da tarar da ake daura wa kan masu dawo da litattafai ba kan lokaci ba a watan Janairun da ya gabata a dukkanin dakunan karatun kasar tun.

''Wannan tunasarwa ce ga duk wadanda ke rike da litattafan dakin karatu da ba su mayar ba har yanzu cewa ''kar su ji tsoro'', a cewar wani ma'aikacin dakin karatun.

Yanzu muna tunanin bayyana litattafan da aka dawo da su tare da lokutan da aka are su.

Labarai masu alaka