Narendra Modi ya sake lashe zaben Indiya

Indian Prime Mininster Narendra Modi during a press conference in New Delhi. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Fiye da mutum miliyan 600 ne suka kada kuri'a a zaben wanda aka gudanar a tsawon mako shida

Firai Ministan Indiya Narendra Modi ya samu sabon wa'adin shekara biyar bayan lashe babban zaben kasar da gagarumin rinjaye a ranar Alhamis.

Sakamakon farko ya nuna cewa jam'iyyarsa ta Bharatiya Janata Party (BJP) za ta lashe kujeru 300 cikin 543 da ke majalisar dokokin kasar.

Babban jam'iyyar adawa wadda Rahul Gandhi ke jagoranta ta amsa shan kaye a zaben.

Mutane suna ganin wannan zaben kamar wani zaben raba gardama a kan manufofin kishin Hindu da firai ministan yake bai wa fifiko.

Fiye da mutum miliyan 600 ne suka kada kuri'a a zaben wanda aka gudanar a tsawon mako shida.

"Na gode Indiya" kamar yadda firai ministan ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ya ce: "Na'am da jama'a suka yi da hadakarmu yana ba mu kwarin gwiwar kara dukufa wajen ganin mun cika musu burinsu."

A lokacin wani taron manema labarai a brinin Delhi ranar Alhamis, jagoran 'yan adawa Mista Gandhi ya amsa shan kaye.

Labarai masu alaka