Ko kirkiro sabbin magunguna zai magance bijirewar da cutuka ke yi masu?

Magunguna Hakkin mallakar hoto SciTech Europa

Kasashe mambobi a hukumar lafiya ta duniya WHO, wadanda ke taron shekara a Geneva, sun goyi bayan matakan da za a sanya da nufin magance matsalar bijirewar da cutuka ke yi wa magunguna, lamarin da ke janyo mutuwar mutane da dama.

Wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar a baya-bayannan ya bayyana cewa bijirewar da cutuka ke yi wa magunguna gagarumar matsala ce ta gaggawa a fadin duniya.

Binciken ya nuna cewa idan ba a dakile ta ba za ta iya haddasa mutuwar mutane miliyan 10 a duk shekara, tare kuma da janyo matsalar tattalin arziki a duniya nan da shekara ta 2050.

Kasashe mambobin hukumar lafiya ta duniyar sun ce ya kamata a dauki wannan matsala a matsayin babban kalubale a harkar kiwon lafiya.

Tuni dai irin wannan matsalar ta bijirewar da cutuka ke yi wa magunguna ta yi sanadiyyar rasa rayukan mutum dubu 700 a shekara guda.

Kasashen sun ce sababbin magungunan da aka fito da su, wadanda za su maye gurbin wadanda cutukan suka bijirewa, babu su a kasuwa kuma ma ba su yi wadatar da za su kawo karshen wannan matsalar ba.

Daga cikin matakan da aka dauka wajen magance wannan matsala sun hada da sanya sharudda a kan duk wani magani da za a yi amfani da shi.

Sannan kuma a kara kudade wajen gudanar da bincike kan sababbin magungunan da za a rika amfani da su idan cuta ta bijire wa wani magani.

Dalilan da ke sa cutuka ke bijire wa magunguna suna da sarkakkiya.

Yawan amfani da magungunan suna rage masu karfi sannan rashin tsafta a asibitoci ko kuma amfani da gurbataccen ruwa na yada wasu cutuka.