Yadda rikicin APC a Zamfara ya samo asali

Gwamna Abdulaziz Yari da dan takararsa kwamishinansa na kudi, Alhaji Muktar Shehu Idris Hakkin mallakar hoto @mancy4real
Image caption Gwamna Abdulaziz Yari da dan takararsa a babban zaben da ya gabata, kwamishinan kudi Alhaji Muktar Shehu Idris

Jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta rabu gida biyu ne, wato bangaren gwamnan jihar mai ci Abdul'aziz Yari da kuma daya bangaren na Mataimakinsa da ministan tsaro da Sanata Marafa da Hon Jaji.

Rikicin na APC a Zamfara ya samo asali ne bayan da Gwamna Abdulaziz Yari ya sanar da goyon bayansa ga kwamishinansa na kudi, Alhaji Muktar Shehu Idris, a matsayin wanda zai gaje shi.

APC a Zamfara ta gaza gudanar da dukkanin zaben fitar da 'yan takararta na gwamna da na yan majalisar tarayya da na jiha.

Wannan ne ya sa wasu daga cikin masu sha'awar takarar gwamnan a jam'iyyar APC su takwas da suka hada da mataimakin gwamnan Ibrahim Wakalla da kuma Ministan tsaro Mansur Dan Ali suka hade kai domin yakar gwamnan na Zamfara.

Sau biyu ana shirya zaben fitar da gwanin a jihar, amma sai a soke saboda rikicin siyasa tsakanin bangarorin jam'iyyar a jihar.

Bangaren gwamnan jihar, ya fake ne da sakamakon wani hukuncin babbar kotun jihar a Gusau, inda alkalin kotun ya ce an yi zabe tare ba hukumar zaben kasar umurnin karbar sunayen 'yan takarar bangaren gwamna da ya yi ikirarin gudanar da zaben.

Hukuncin wata babbar kotun tarayya a Abuja, ya tabbatar da matsayin hukumar zaben kasar na haramta wa duk 'yan takarar jam'iyyar APC daga Zamfara shiga zabukan kasar da za a yi cikin watan gobe da na jibi.

Hukuncin ya ci karo da na kotun jihar karkashin mai shari'ah Muhammad Bello Shinkafi.

Sai dai mai shari'a Ijeoma Ojukwu ta kotun tarayya ta jaddada matsayin INEC inda ta ce jam'iyyun siyasa za su ci gaba da yin karan-tsaye ga ka'idojin zabe muddin suka kasa mutunta sharuddan da aka shata na jadawalin zabe.

Kotun ta ce hukuncin darasi ne ga sauran jami'yyun siyasa a nan gaba.

Bayan dage zaben 2019 ne wata kotu a Abuja ta ba hukumar zabe umurnin ta karbi 'yan takarar jam'iyyar APC, matakin da ya sa APC ta shiga zabukan 2019 a Zamfara.

Wata kotun daukaka kara a Sokoto ce kuma ta soke hukuncin umarnin da kotun Abuja ta bayar, inda kuma bangaren gwamnati ya daukaka kara zuwa kotun koli.

Yanzu kuma Kotun Koli ta soke zaben 'yan takarar jam'iyyar ta APC baki daya.