Abubuwan da ba ku sani ba game da 'Singham'

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
CP Singham, dan Sanda abokin kowa

Latsa hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon

Taken dan sanda abokin kowa ya zo daidai da Wakili ganin yadda jama'a da dama ke bayyana irin yadda yake bai wa kowa girmansa daidai gwargwado tun daga kan jami'an 'yan sanda har zuwa jama'ar gari.

Shi ne dan sandan da jama'a ke bin ayarin motocinsa saboda kyakkyawan zato da jama'a ke yi masa na kamanta gaskiya, kamar yadda tawagar BBC Hausa ta shaida hakan a wata ziyara da ta kai masa.

Mohammed Wakili, dan sanda ne mai kwarjini wanda ya yi fice a Najeriya musamman inda ake yabon shi da kamanta gaskiya.

A yanzu haka dai, dan sandan ya yi ritaya daga aikin dan sanda a ranar Juma'a 24 ga watan Mayun 2019, kwanaki biyu kafin cikarsa shekaru 60 da haihuwa.

Lakabin Singham

Image caption CP Wakili yana da farin jini a wajen 'yan sandan da ke karkashinsa

Irin hazakar da Wakili ke nunawa ta sa har jama'ar gari suka yi mashi lakabi da 'Singham,' wanda suna ne na wani jajirtaccen dan sanda a wani fim din Indiya.

Ganin yadda wannan suna da aka lakaba masa ya bi duniya, shi ma Wakili ya amince a rika kiransa da wannan suna.

Mohammed Wakili ya fara yin fice a Najeriya ne tun bayan wani bidiyo da ya watsu a shafukan sada zumunta inda aka nuno shi yana nuna kiyayya tsantsa ga fatauci da shan miyagun kwayoyi da kuma daba a tsakanin al'umma.

Yaduwar bidiyon ce ta sa aka fara sanin CP Wakili, inda a lokacin yake matsayin Kwamishin 'yan sanda na jihar Katsina.

Alamu sun nuna cewa yaki da Wakili yake yi da sha da fataucin miyagun kwayoyi da kuma ta'addanci da gaske yake yi ganin yadda ya kama dillalan makamai da na kwaya da 'yan kwayar kansu a zamansa da ya yi a Katsina da Kano.

Wakili ya kara yin suna lokacin zaben shugaban kasa da kuma na gwamna a Kano inda ya yi tsayuwa irin ta masu daka wajen ganin cewa an yi zabe lafiya.

Amma kash! a daidai lokacin da tauraruwar Wakili ke haskawa abun da ya rage masa makwanni kadan ne ya yi ritaya.

Babban abin da mutane suka so shi ne Wakili ya kai kololuwa a aikin 'yan sanda sakamakon irin jajircewa da kuma kwarewa da ya ke nunawa wajen gudanar da aikinsa.

Duk da cewa a baya yana nuna irin wannan kwarewa da kuma kamanta gaskiya, amma sai a wannan lokaci ne za a iya cewa Wakili ya yi suna a idon duniya.

Takaitaccen tarihin rayuwar CP Wakili

An haifi Mohammed Wakili a ranar 26 ga watan Mayun 1959 a garin Gombe.

Ya yi makaranatar firamare a Central Primary School da ke Gombe inda ya gama a 1973, sai kuma bayan nan ya tafi makarantar sakandare ta Government Secondary School da ke Maiduguri inda ya samu shaidar kammala karatun sakandare ta SSCE a 1977.

Daga nan sai ya tafi jami'ar Maiduguri ya kammala karatunsa na digiri kan Hausa da kuma harsuna a 1985, daga nan ne kuma ya tafi aikin yi wa kasa hidima inda ya kammala a 1986.

Bayan ya gama hidimar kasa ne ya tsunduma aikin dan sanda inda ya shiga makarantar horar da jami'an 'yan sanda ta Najeriya daga 1988 zuwa 1989.

Aikin dan sanda

Image caption Wakili tare da ma'aikatan BBC, Yusuf Ibrahim Yakasai da Halima Umar Saleh a wata ziyara da suka kai masa

Bayan Wakili ya kammala makarantar horar da 'yan sanda a 1989, ya fara aikinsa ne a matsayin ASP a hukumar 'yan sanda da ke Bauchi.

Sai a shekarar 1993 ya koma Legas inda ya ci gaba da aiki a sashen ilimi na hukumar 'yan sanda wanda daga baya kuma ya koma bangaren tattara bayanan sirri da bincike na hukumar a jihar ta Legas.

A 1997, ya tafi kasar Angola domin gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya.

A shekarar 2000 ne aka mayar da shi rundunar 'yan sanda da ke reshen jihar Anambra inda ya shafe shekara daya, daga baya kuma aka mayar da shi jihar Kano a shekarar 2001.

A 2003 ya koma jihar Legas bangaren tattara bayanan sirri na hukumar 'yan sandan sai kuma daga nan ya koma hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa EFCC.

Kafin Wakili ya koma Kano a farkon shekarar 2019, ya yi zama a shelkwatar hukumar 'yan sandan da ke birnin tarayya Abuja da kuma kuma jihar Katsina.

Wakili ya yi ritaya ne a ranar Juma'a 24 ga watan Mayun 2019.

A yanzu haka Wakili na da mata daya da 'ya'ya 17 da jika daya.

Kwarewa

Wakili ya samu horo daban-daban musamman a harkar tsaro tun daga shigarsa aikin dan sanda a 1989.

'Yan sanda da dama a Najeriya sun yi kaurin suna wurin hada baki da masu mulki a lokutan zabe inda ake zarginsu da muzgunawa 'yan adawa, lamarin da suka sha musantawa.

Sai dai Mohammed Wakili wanda aka tura shi jihar Kano jim kadan kafin zaben, kawo yanzu ya ciri tuta.

Kusan baki yazo daya tsakanin al'umma wurin yabawa rawar da yake takawa ta yakar 'yan bangar siyasa, da daba, da kuma nuna ba-sani-ba-sabo a huldarsa da 'dukkan bangarorin siyasar kasar.

Rahotanni sun ce an yi kokarin sayensa da kudi domin ya bari a yi magudi amma ya yi ki amincewa.

Sai dai a wani bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta na wani jawabi da ya yi a wani wurin tattara sakamakon zabe, ya ce ai shi "ba wanda zai kuskura ya tunkare shi da cin hanci.

"Tsayuwar-dakan da ya yi ya fito fili ne bayan da jami'ansa suka cafke manyan jami'an gwamnati bayan da aka zarge su da kawo cikas wurin bayyana sakamakon zaben karamar hukumar Nassarawa.''

Wannan ya sa sunansa ya zama daya daga cikin maudu'an da aka rinka tattaunawa a kansu a shafukan sada zumunta, inda mutane suka rinka yaba masa.

Sai dai ba a ji duriyarsa ba a lokacin da aka zo kammala zaben a ranar 23 ga watan Maris, duk da irin tashin hankalin da aka samu a mafi yawan wuraren da zaben ya gudana.

Wasu kafafen yada labarai sun ruwaito cewa hakan ba zai rasa nasaba da "kwace ikon da aka yi daga hannunsa ba inda aka mika komai ga mataimakin sufeto janar da wasu manyan jami'ai da aka tura jihar daga Abuja".

Image caption Wakili a ranarsa ta karshe a matsayin dan sanda.

Labarai masu alaka