Abin da ya sa muka zartar da hukuncin kisa - Masari

FACEBOOK/BUHARI SALLAU Hakkin mallakar hoto FACEBOOK/BUHARI SALLAU

Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa masu garkuwa da mutane da barayin shanu za su fuskanci hukuncin kisa idan aka same su da laifi.

Gwamnatin ta bayyana hakan ne bayan gyaran da aka yi wa kundin shari'a na penel code na jihar.

Hakazalika, gyaran dokar ya hada da daurin rai da rai ga duk wanda aka kama da laifin fyade inda mutum zai kuma biya diyya.

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bayyana cewa, matakin da suka dauka na mayar da satar shanu da garkuwa da mutane manyan laifuka ya biyo bayan kara ta'azzara na irin wadannan laifuffukan da ake samu a jihar.

Jihar Katsina dai na cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da rashin tsaro musamman fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.

Sakamakon matsalar rashin tsaro a jihar, ko a kwanakin baya sai da gwamnan jihar ya yi hasashen cewa za a yi karancin abinci a jihohin da ake satar mutane ganin cewa jiharsa na daga cikin jihohin da ke fuskantar wannan matsalar.

Ganin irin yadda 'yan bindiga ke kashe mutane musamman a kauyukan da ke kewaye da jihar kamar su Safana da Batsari da wasu yankunan ya sa gwamnan ya yi takakkiya zuwa ga shugaban Najeriya domin neman agaji da kuma nemo mafita ga yadda za a shawo kan matsalar.

Wannan na zuwa ne bayan harin da aka kai a kauyukan Dan Tsunsu da Na huta da kuma 'yan Kura da ke cikin karamar hukumar Safana a ranar Laraba.

Hare-haren 'yan bindiga da satar mutane don kudin fansa na ci gaba da karuwa a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna duk da yunkurin jami'an tsaro na kawo karshen matsalar da ta addabi yankin arewa maso yammacin kasar.

Mutane da dama ne dai suka rasa rayukansu, yayin da yara da dama suka kasance marayu sakamakon kashe-kashen da ke faruwa a jihohin.

Labarai masu alaka