Gobara ta kashe dalibai da dama a wata makaranta a Indiya

Fire rips through Gujarat college Hakkin mallakar hoto Getty Images

Akalla mutum 20 ne suka mutu wadanda akasarinsu dalibai ne a wata gobara da ta kama wasu dakunan karatu da ke wata makaranta a birnin Surat da ke Indiya.

Hukumomi a kasar sun bayyana cewa, an ga dalibai suna tsalle daga saman ginin makaranatar suna fadowa kasa sakamakon babu hanyar da za su bi su sauko kasa saboda tsananin wutar da ta kama.

Ana ganin cewa wutar ta samo asali ne sakamakon matsalar wuta da daya daga cikin na'urar sanyaya daki ta makarantar ta samu.

'Yan sandan Surat sun bayyana cewa a yanzu haka an kama daya daga cikin wadanda suka mallaki makarantar.

Shugaban 'yan sandan Surat wato Satish Sharma ya bayyana wa manema labarai cewa, ana zargin mutum uku da zargin kisar kai amma an riga an kama mutum daya cikinsu kuma ana daf da kama sauran biyun.

Ya kuma ba al'ummar yankin hakuri da kada su dauki doka a hannunsu ganin yadda suka fusata bayan faruwar lamarin.

Akalla mutum 20 ne suka samu raunuka kuma an bayyana cewa ana kula da su a asibitin da ke jihar Gujarat da ke kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa duk wadanda suka mutu 'yan kasa da shekara 20 ne kuma sun kasa fita ne sakamakon wutar ta fara ne ta matattakalar hawa ginin makarantar.

Firai ministan kasar Narendra Modi, ya aika da sakon ta'aziyya a shafinsa na Twitter dangane da faruwar lamarin.

An kafa kwamitin bincike da zai yi bincike kan wannan gobarar kuma ana sa ran bayan kwanaki uku kwamitin zai gabatar da rahoto.

Wannan na daga cikin jerin iftila'in gobara da aka samu a Indiya inda a watan Fabrairu ma akalla mutum 17 suka mutu a wata gobara da ta faru a wani Otel da ke Delhi.

Labarai masu alaka