Zan magance matsalar tsaro a jihar Zamfara - Bello Matawalle

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Gwamnan mai jiran gado ya ce ya san matsalolin jihar Zamfara

Bayan tabbatar masa da nasara, gwamnan jihar Zamfara mai jiran gado, Muhammad Bello Matawalle ya ce rashin adalci na daga manyan dalilan da suka haifar da rashin tsaro a jihar Zamfara.

Sabon gwamnan wanda tsohon shugaban kwamitin tsaro ne na majalisar wakilai ta Najeriya, ya ce kwarewarsa ta sa ya fahimci hanyoyin da zai bi wajen kawo karshen matsalar tsaro da jihar ke fama da ita.

A ranar Asabar ne hukumar zabe ta Najeriya INEC ta bayyana Bello Matawalle na jam'iyyar PDP a matsayin zababben gwamnan Zamfara.

Shugaban hukumar zaben Mahmud Yakubu ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja inda ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ita ce ta yi nasara a dukkanin guraben jihar sai dai an samu gurbi daya na majalisar jiha inda dan jam'iyyar NRM wato Kabiru Hashimu ya lashe kujerar mazabar Maru ta kudu.

Ya ce wannan na zuwa ne bayan hukuncin da kotun koli ta yanke a ranar Juma'a inda ta soke guraben dukkanin 'yan takarar jam'iyyar APC na jihar.

A hukuncin da kotun ta bayar, ta bayyana cewa jam'iyyar APC ba ta gudanar da sahihin zaben fitar da gwani ba wanda hakan ya yi sanadiyar soke kuri'un da jam'iyyar ta samu a zaben 2019 a jihar.

A zaben da aka gudanar na gwamna a jihar, Bello Matawalle ne ya zo na biyu da kuri'u 189,452 wanda a yanzu haka shi ne na daya.

A ranar Juma'a ne kotun kolin Najeriya ta yanke hukunci inda ta ce jam'iyyar APC ba ta yi zabukan fitar da gwani ba, don haka jam'iyyar da take bin APC a yawan kuri'u ita ce ta lashe zabukan jihar da aka yi a watan Maris.

Hukuncin kotun ya jaddada hukuncin da kotun daukaka kara a jihar Sokoto ta yanke, wadda ita ma ta yanke hukuncin cewa jam'iyyar APC ba ta gudanar da sahihin zaben fidda gwani ba a jihar.

A hirarsa da BBC, gwamna mai jiran gado ya ce zai hada kai da gwamnatin tarayya ta APC wajen kawo zaman lafiya a jihar Zamfara.

Ya kuma bayyana cewa a wa'adin mulkinsa zai zauna ne a jihar Zamfara duk wuya duk dadi.