'Ba ma bukatar dakarun kasashen waje a Nijar'

Zanga- Zangar dalibai a Nijar Hakkin mallakar hoto Newsweek

Babbar kungiyar daliban Jamhuriyar Nijar, ta gudanar da wani tattaki na musamman zuwa harabar majalisar dokokin kasar da ke Yamai a ranar Asabar.

Daliban sun yi hakan domin nuna goyon baya ga jami'an tsaron kasar da ake kai wa hare-haren ta'addanci da kuma yin kira ga 'yan kasar da su kula da matsalolin da suka yi wa bangaren ilimi tarnaki.

Kazalika daliban, sun yi kira ga gwamnatin kasar ta Nijar da ta kori dakarun kasashen turai da ke cikin kasar ba tare da bata lokaci ba.

Shugaban kwamitin zartarwa na kungiyar daliban Amadou Arifa Hassan, ya shaida wa BBC cewa, baya ga nuna goyon baya ga dakarun kasar ta su, sun yi kuma tattakin ne domin nuna alhini da bakin cikinsu game da kashe sojojin kasar da aka yi a kwanakin baya.

Amadou Arifa Hassan, ya ce a bangaren ilimi ma, akwai babban kalubale domin kuwa a cikin tattakin na su sun yi kira ga gwamnatin kasar da ta kara kokari wajen farfado da bangaren ilimi domin kuwa an yi watsi da shi.

Ya ce sanin kowa ne, sai da aka shafe wata hudu ba a karatu a jami'oin kasar saboda yajin aikin da malaman jami'oin suka shiga.

Dalibin ya ce a harkar tsaron kasar ma akwai babban gyara domin kuwa dakarun kasashen waje da ke a kasar da aka jibge ba su ga wani aiki da suke yi ba duk da makaman da suke da su, tun da dai duk da kasancewar ta su a kasar ba a fasa kai hare-hare da kuma kashe-kashen ta'addancin da ake yi ba a wasu wurare na kasar.

Don haka ya ce ' Mu abin da muke so shi ne gwamnati ta sanar da su cewa su tattara na su ya nasu su koma kasashensu'.

Amadou Arifa Hassan, ya ce ko da wasa sojan Nijar ba zai je Faransa a bar shi ya zauna har ya yi abin da ya ga dama a kasar ba, amma me ya sa su a kasarsu za a kyale sojojin wasu kasashen su zauna musu a kasa.

Ya ce yanzu sun ringa sun shaida wa gwamnati bukatarsu, don haka za su sanya idanu suga ko gwamnatin za ta yi wani, idan ba ta yi ba, to su za su san abin yi.

Labarai masu alaka