Zaben da muka yi mun yi kura-kurai - Gwamna Yari

Gwamna Abdulaziz Yari Hakkin mallakar hoto FACEBOOK
Image caption Gwamna Yari ya yi wa gwamnatin da za ta gaje shi Addu'a

Gwamnan Zamfara mai barin gado Abdulaziz Yari Abubakar ya amince da hukuncin kotun koli tare da yi wa wanda zai gaje shi fatan alheri.

A yayin da yake jagorantar shan ruwan azumin ramadan na karshe tare da kwamishinoni da manyan kushoshin gwamnatinsa a gidansa da ke Talatar Mafara gwamnan ya ce "mun aminta kuma mun yadda da hukuncin Ubangiji."

A ranar juma'a ne kotun koli ta yanke hukuncin cewa jam'iyyar APC ba ta yi sahihin zaben fitar da gwani ba wanda hakan ya yi sanadin soke kuri'un da jam'iyyar ta samu a dukkanin kujerun da ta lashe a zaben 2019 a jihar.

Hukumar INEC kuma ta tabbatar da 'yan takarar jam'iyyar PDP da suka zo na biyu a matsayin wadanda suka lashe zaben na gwamna da na 'yan majalisar Tarayya da na jiha.

Da yake jawabi, Gwamna Yari ya amsa cewa zaben da aka yi akwai kura-kurai a ciki, inda ya ce sun yadda da hukuncin kotun koli, "wannan tsari ne wanda Allah ya riga ya tsara haka."

"Imanin mutum ba ya cika sai ya yi imani da kaddara alheri ko sharri,"

"Wannan yana cikin sharadin cewa imaninmu ya cika," in ji shi.

Gwamna Yari ya kuma yi wa gwamnatin da za ta gaje ji addu'ar fatan alheri, inda ya ce yana fatan Allah zai ba su ikon yin adalci.

"Allah ya masu jagora ta hanyar da jihar Zamfara za ta ci gaba da kuma hanyar da al'umma za su ci gaba."

An ta yada hoton bidiyon jawabin gwamnan a kafofin sada zumunta na intanet.

INEC ta fitar da jerin sunayen zababbun 'yan takara a Zamfara

Gwamna da mataimaki

'Yan majalisar dattawa

'Yan majalisar Wakilai

Labarai masu alaka