Iraki ta yanke hukuncin kisa ga 'yan IS 'yan kasar Faransa

Reuters Hakkin mallakar hoto Reuters

Wata kotu a Iraki ta yanke wa wasu maza uku 'yan kasar Faransa hukuncin kisa bayan samun su da laifin shiga kungiyar IS.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa mazan da aka yanke wa hukuncin sun hada da Kévin Gonot da Léonard Lopez da kuma Salim Machou.

An bayyana cewa suna da kwanaki 30 su daukaka kara.

Wadanda aka yanke wa hukuncin na daga cikin 'yan kasar Faransa 12 da sojojin Amurka suka kama a Syria.

A watan Fabrairu ne aka mayar da wadanda ake zargin zuwa Iraki domin fara sauraren karar da aka shigar kansu.

Wadanda aka yanke wa hukuncin su ne 'yan kasar Faransa na farko da ake zargi da shiga kungiyar IS da aka fara yanke wa hukuncin kisa.

Har yanzu dai Faransa bata ce komai ba dangane da hukuncin da kotun kasar Syriar ta yanke ba. Amma da aka matsa lamba kan lamarin a watan Fabrairu, Shugaban Faransar Emmanuel Macron ya ki cewa komai dangane da lamarin sai dai ya ce lamari ne da kasar Iraki ke da iko a kai.

Tuni dai kungiyoyin kare hakkin bil adama suka soki wannan shari'ar inda suka bayyana cewa kotun ta dogara ne da hujjojin da ta samu ne bayan an tilasta wa wadanda ake zargin da su amsa laifinsu karfi da yaji.

Su wane ne ake zargi?

Gonot mai shekaru 32 ya fito ne daga kudu maso gabashin Faransa. Ana ganin cewa ya shiga Syria ne ta kasar Turkiyya inda ya shiga kungiyar al-Nusra, wacce wani reshe ne na al-Qaeda kafin ya yi mubaya'a ga kungiyar IS.

Macou, mai shekaru 41 na daga cikin reshen 'yan kungiyar IS din da ta kunshi mayaka 'yan asalin kasashen Turai da suka kai hare-hare Iraki da Syria inda kuma suka shirya kai wasu hare-haren a Brussels da kuma Paris kamar yadda wata cibiyar bincike kan tsaro ta ''Centre d'Analyse du Terrorisme'' ta bayyana.

Lopez, mai shekaru 32 wanda dan asalin kasar Faransa ne, ya koma da zama garin Mosul shi da iyalinsa kafin shiga Syria kamar yadda wasu masu bincike na kasar Faransa suka bayyana.

Lauyansa, Nabil Boudi ya yi watsi da wannan hukuncin da kotun ta yanke inda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, ''wannan hukuncin an yi shi ne bisa irin tilasta wa wadanda ake zargin amsa laifinsu a gidajen yarin da ke Bagadaza''

Labarai masu alaka