Abubuwa hudu da za su faru a wannan makon

Yau take Litinin wadda ke nuni da cewa mun shiga sabon mako. Duk da cewa ba mu san duka abubuwan da za su faru a wannan makon ba, amma akwai batutuwan da muke hasashen su ne za su iya faruwa a makon.

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da muke sa ran za su faru a makon.

1-Rantsar da Shugaba Buhari

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaban ya fara wa'adin mulkinsa na farko ne a shekarar 2015

A ranar Laraba ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai sake shan rantsuwar wa'adinsa na biyu, bayan ya lashe zaben watan Fabrairun shekarar 2019.

Za a rantsar da shi ne a dandalin Eagle Square da ke Abuja.

Shugaban ya fara wa'adin mulkinsa na farko ne a shekarar 2015.

2- Za a rantsar da gwamnoni 29

Hakkin mallakar hoto Facebook/Nigeria Guradian
Image caption Za a rantsar da gwamnonin ne a jihohi 29

Haka zalika za a rantsar da gwamnoni wadanda suka lashe zaben gwamnoni da aka gudanar a Najeriya a watan Maris da ya gabata.

4- Ranar Kudus

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Juma'ar wannan mako ce ta karshe a cikin watan Ramadan na bana, inda ake saran mabiya Shi'a za su yi tattaki don tuna wa da ranar Kudus kamar yadda suka saba yi duk shekara.

Akan yi irin wannan tattaki ne da manufar nuna juyayi dangane da subucewar da masallacin baitul maqdis da ke birnin Qudus ya yi daga hannun musulmi.

4- Gasar Zakarun Turai ta Europa

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A ranar Laraba ne za a san Zakarun Gasar Europa na bana, bayan Chelsea ta fafata da Arsenal a filin wasa na ‎Baku da ke kasar Azerbaijan.

Chelsea ta samu damar zuwa Gasar Zakarun Turai bayan ta kare a matsayi na uku, yayin da Arsenal take fatan doke Chelsea a Gasar Europa don ta samu damar ci gaba Gasar Zakarun Turan.

5- Gasar Zakarun Turai ta Champions League

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Har ila yau, za a san zakara tsakannin Tottenham da Liverpool a Gasar Zakarun Turai ta Champions League bayan sun fafata a filin wasa na Wanda Metropolitano da ke birnin Madrid a kasar Spain ranar Asabar.

Labarai masu alaka