Ya kamata mutane su daina biyan kudin fansa - Masari
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A daina biyan masu garkuwa kudin fansa – Masari

Latsa hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya nemi jama'a da su daina ba wa masu garkuwa da mutane kudin fansa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a fadar shugaban kasar Najeriya bayan da Buhari ya gana da gwamnoni a ranar Litinin.

Sun yi ganawar ne cikin sirri a Abuja, taron ya fi mayar da hankali kan matsalar masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa da kuma batun Boko Haram.

Labarai masu alaka