An haramta fitar da kayan lambu daga Ghana

Tattasai Hakkin mallakar hoto Getty Images

Hukumomi a Ghana sun dakatar da fitar da kayan lambu da suka hada barkono da yalo sakamakon fargabar da ake yi na suna dauke da kwayoyin cuta ko kuma tsutsa.

Ma'aikatar noma da abinci ta kasar Ghana ta bayyana cewa dokar haramta fitar da kayayyakin da aka kafa, za ta fara aiki ne daga mako mai zuwa kuma dokar za ta ci gaba har sai abin da hali yayi.

Wannan dakatarwar na zuwa ne a daidai lokacin da Kungiyar Tarayyar Turai ta ba kasashen dake shigar mata da kayayyaki umarnin bayar da rahoto kan yadda suke kula da kwayoyin cuta masu illa ga irin wadannan kayayyakin.

Kungiyar manoma da kuma masu fitar da kayayyakin lambu ta kasar Ghana ta bukaci gwamnatin kasar ta daga wannan dokar, inda ta bayyana cewa dokar za ta jawo matsala ga manoma kusan dubu hudu.

Amma hukumomi a kasar sun ki amincewa da haka inda suke tsoron kada Kungiyar Tarayyar Turan ta kara saka masu takunkumi ganin cewa ba a dade da cire masu takunkumin da aka saka masu kan shigar da kayan lambu ba a bara.

Labarai masu alaka