Mun yi nasara a harkar tsaro – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto TWITTER/ BASHIR AHMAD
Image caption Gwamnatin Buhari na ikirarin cewa ta ci lagon 'yan kungiyar Boko Haram

Gwamnatin Najeriya ta ce ta gamsu da irin nasarar da ta samu kawo yanzu a yunkurin da take yi na magance matsalar tsaro da ta addabi kasar.

Babban mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin watsa labarai, Mallam Garba Shehu ne ya bayyana haka a wata hira da BBC.

Ya ce: ''Lokacin da muka shigo ai babbar matsala ta tsaro a kasar ita ce ta Boko Haram.

Bama-bamai da kashe-kashe a birane da kauyuka, amma a yau wannan matsala ta koma can kan iyakar Najeriya da Tafkin Chadi.

Kuma a hakan ma ana kokari a ga an yi maganinta gaba daya.''

Kakakin ya kara da cewa, matsalar fadace-fadace tsakanin manoma da makiyaya, ita ma ta lafa yanzu, domin idan aka duba jihohin Filato da Binuwai da Nasarawa inda abin ya zafafa, su ma sun yi sauki in ji shi.

Garba Shehun ya kuma ce, sabuwar matsalar da ta taso wadda ya ce ita ma tun a da akwai ta, amma yanzu ta tsananta, ta satar mutane domin karbar kudin fansa da kashe-kashe, ita ma gwamnati ta tashi tsaye domin magance ta.

A ranar Laraba ne 29 ga watan Mayu za a rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari a wa'adi na biyu a kan mulki.

Sai dai `yan kasar sun samu kansu a wani mawuyacin hali ta fuskar tsaro kafin da kuma har zuwa lokacin hawansa mulki a shekara ta 2015, sakamakon hare-haren da kungiyar Boko-Haram ke kaiwa, inda mutane da dama suka mutu.

Tare kuma da bannata dukiya mai yawa da raba wasu dimbin jama'ar da muhallansu, abin da ya tilasta wa wasu gudun hijira a ciki da wajen kasar.

Kuma wannan ne ya sa alkawarin inganta tsaro da Shugaba Buharin ya yi a lokacin da yake yakin neman zabe kafin wa'adinsa na farko, ya ja hankalin `yan kasar da dama.

Duk da cewa tsaro ya inganta a farkon hawansa karagar mulki, musamman ma a shiyyar arewa-maso-gabashin kasar, wata masifar da ta barke ta satar mutane a wasu sassan kasar ta sa wasu na ganin cewa gwamnatinsa ta gaza wajen cika alkawarin da ta dauka.