Za a rantsar da Peter Mutharika sabon wa'adin mulki a Malawi

Peter Mutharika Hakkin mallakar hoto AFP

Za a sake rantsar Shugaban kasar Malawi Peter Mutharika a sabon wa'adin mulki na biyu bayan ya lashe babban zaben kasar.

Za a yi bikin rantsar da shi ne a babban birnin kasuwancin kasar wato Blantyre sa'o'i kalilan bayan sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben kasar.

Mista Mutharika, wanda ya fara shugabancin kasar ne a shekarar 2014, bayan ya samu kaso 38.5 cikin 100 na kuri'un da aka samu.

Wanene Peter Mutharika?

Peter Mutharika lauya ne kuma malami a tsangaya koyar da aikin shari'a.

Bayan komawarsa gida a shekarar 2008 na an nada shi mai ba dan uwansa Bingu wa Mutharika shawara na musaman kan harakokin shari'a lokacin dan uwan na shugaban kasa.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Peter Mutharika lauya ne kuma malami a tsangaya koyar da aikin shari'a

Bayan mutuwar shugaban kasar a shekarar 2012 wanda ya mutu ta dalilin bugun zuciya ya shugabanci jam'iyyar mai milki ta DPP daga shekarar 2012.

Sai dai mataimakiyar shugaban kasar ce Joyce Banda ta gaji Bingu wa Mutharika kan ragamar milkin kasar har zuwa shekarar 2014.

A shekara ta 2013, an kama shi bisa zarginsa da shirya makalkashiya don kifar da Shugaba Joyce Banda.

Kotu ta zarge shi da yunkurin boye gawar dan uwansa da kuma hana mataimakiyar shugaban kasar ta gaje shi kamar yadda tsarin mulki ya tanadar.

Ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a 2014 da sama da kashi 36 cikin 100 na kuri'un da aka jefa.

Labarai masu alaka

Karin bayani