An rantsar da Shugaba Buhari a wa'adi na biyu

Getty Images Hakkin mallakar hoto Getty Images

A ranar 29 ga watan Mayun 2019 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sha rantsuwar fara aiki ta wa`adin mulkinsa na biyu na shekara hudu.

''Next Level,'' wato mataki na gaba a Turance, shi ne taken yakin neman zaben shugaban kasar, a babban zaben da ya wuce, kuma taken ya cusa wa `yan kasar fatan cewa za su ga sauyi a harkar shugabanci a kasar, sakamakon matsalar tsaro da matsin tattalin arziki da aka fuskanta a wa`adin da ya shude.

Amma wani furucin da shugaban kasar ya yi cewa akwai jan-aiki a gaba ya sa wasu na fassara mataki na gaban ta fuskoki daban-daban, har ma wasu na cewa watakila wata sabuwar wahalar ce za a yi fama da ita.

Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Muhammadu Buhari mai shekara 76 - mutum ne da ake yi masa kallon tsayayye a kan akidarsa.

Duk da shan kaye da ya yi a zabuka uku da suka gabata, amma ya sami nasara a zaben 28 ga watan Maris din 2015, inda ya zama dan hamayya na farko da ya sami galaba a kan shugaban da ke kan karagar mulki.

Buhari ya kara da Shugaba Goodluck Jonathan, wanda dan yankin Neja Delta ne kuma Kirista daga kudancin kasar.

A 2015, ya yi sa'ar samun goyon bayan gamayyar jam'iyyun siyasar Najeriya mai suna All Progressives Congress (wato APC).

A wannan karon ma, ya fito karkashin inuwar jam'iyyar ta APC din ne inda ya kara da tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar na babbar jam'iyyar hamayya ta PDP ya kuma samu nasara a kansa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Sa rai da samun sauyi

Bayan da shugaban ya dare mulki a 2015, 'yan Najeriya da dama sun sa rai da samun sauyin rayuwa, ta bangaren ingantuwar tsaro da tattalin arziki da magance cin hanci da rashawa.

Sai dai masu sharhi kan al'amuran yau da kullum sun sha cewa shugaban bai yi wani abin a zo a gani ba ta bangaren tattalin arziki.

To amma shugaban na samun yabo ta bangaren magance rikicin Boko Haram, duk da cewa wasu na ganin da sauran rina a kaba a fannin.

A bangaren tsaron dai, akwai matsalar garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da ake fama da ita musamman a arewa maso yammacin Najeriyar.

Idan kuma aka tabo batun tattalin arziki kuwa, masu sharhi da dama na ganin babu wani cigaba da aka samu.

Fatan 'yan Najeriya a wa'adi na biyu

'Yan Najeriyar da dama na fatan samun sauki musamman ga halin matsi na rayuwa da kuma saukin tsaro a wasu sassa na kasar.

Wasu na ganin cewa shugaban a baya ya yi iya bakin kokarinsa wajen shawo kan matsalar sai dai har yanzu, akwai sauran jan aiki a gabansa.

Babban burin wasu kuma shi ne samun sauki wajen tattalin arziki. 'Yan kasar na kokawa game da tsada na kayan masarufi da dai sauransu.

Rashin lafiya

Shugaba Buhari ya shafe tsawon lokaci yana jinya a shekarar 2017, inda har ya shafe sama da kwana 100 yana jinya a Birtaniya.

Wannan al'amari ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a ciki da wajen kasar.

A lokacin, rudani ya yawaita kan halin da shugaban ke ciki ganin cewa ba a samu jin ta bakin makusantansa game da ainahin abin da ke damun shugaban ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Bayani kan Shugaba Muhammadu Buhari a takaice:

  • Shekararsa 76
  • An zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 28 ga Maris 2015
  • Ya yi shugaban mulkin sojan Najeriya daga 1984 zuwa 1985
  • An hambare shi a juyin mulki
  • An yi amanna ba shi da cin hanci da rashawa
  • Musulmi ne daga arewacin Najeriya
  • Ya tsallake rijiya da baya a wani hari da Boko Haram ta kai masa a Kaduna
Hakkin mallakar hoto Getty Images

Akwai bambamcin ra'ayi game da tasirin mulkin sojin Buhari na watanni 20 da ya yi.

Kimanin 'yan siyasa 500 da ma'aikata da 'yan kasuwa ne aka tsare a kurkuku a lokacin wannan yaki na almubazzaranci da cin hanci da rashawa.

Wasu mutane suna ganin hakan a matsayin yin amfani da karfin soji da ya wuce misali.

Wasu ko suna tuna wannan lokacin a matsayin wani yunkurin yaki da cin hanci da ya ki ci ya ki cinyewa, abin da ya dakile cigaban Najeriya.

A dalilin wannan ne 'yan siyasa har ma da sojoji da farar hula suka shaide shi da halin gaskiya da rikon amana.

Daya daga cikin abubuwan da ya yi shi ne bai wa 'yan Najeriya umarnin bin layuka a tasoshin shiga mota da bankuna da sauransu, kana ya tura sojoji masu ladabtar da wadanda ke kin bin doka.

An dinga ladabtar da ma'aikatan gwamnati da aka kama su da zuwa wurin aiki a makare ta hanyar sanya su yin tsallen kwado.

Ya kuma gabatar da wata doka mai tsauri ta sanya wa 'yancin 'yan jarida takunkumi, inda har aka daure wasu 'yan jarida biyu a lokacin mulkin sojansa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A hannu guda kuma, kokarinsa na farfado da tattalin arziki inda ya dakatar da shigo da kayayyaki daga kasashen waje ya jawo mutane da dama sun rasa ayyukan yi tare da durkushewar kasuwancinsu.

Farashin kayayyaki ya tashi inda rayuwa ta sauya, wanda hakan ya sanya Janar Ibrahim Babangida ya yi masa juyin mulki ranar 27 ga watan Agustan 1985. An daure Buhari a kurkuku na tsawon wata 40.

Janar Babangida ya so ya yi gaggawar bai wa farar hula mulki, wanda Janar Buhari bai dauki hakan da muhimmanci ba.

Labarai masu alaka