Kamel Eddine Fekhar: Mai fafutuka ya mutu bayan ya yi yajin cin abinci

Zanga zanga a garin Alges biyo bayan mutuwa Kamel Eddine Fekhar Hakkin mallakar hoto AFP/Getty Images
Image caption An yi zanga-zanga a birnin Algiers biyo bayan mutuwar Kamel Eddine Fekhar

Kamel Eddine Fekhar ya fara yajin kin cin abincin ne bayan da aka tsare shi a wani gidan yarin da ke garin Ghardaïa, a kudancin babban birnin kasar Aljeriya tun ranar 2 ga watan Afrilun da ya gabata.

An kama Kame tun ranar 31 ga watan Maris tare da abokin gwagwarmayarsa, Hadj Brahim Aouf bayan ya yi wata hira ta bidiyo, inda ya nuna rashin amincewa da irin abubuwan da ake wa 'yan kabilar Mozabite.

An tura Kamel zuwa asibiti don samun kulawa ganin jikinsa ya tsananta.

A cewar wani na kusa da iyalansa ya kamu da mummuna rashin lafiya, don ya ma shiga cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai kafin ake kai shi asibiti.

Mutuwarsa ta janyo ka ce na ce a kafofin sada zumunta.

Kungiyoyin kare hakin dan Adam sun bukaci a yi bincike don gano musababin mutuwarsa.

A watan Disimbar shekarar 2016 , wani dan jarida dan kasar Aljeriya Mohamed Tamalt shi ma ya rasa ransa, bayan da ya kwashe watanni uku yana yajn kin cin abinci a wani gidan yarin da ake tsare da shi inda zai kwashe shekaru biyu bisa laifin aikata ba daidai ba ga shugaban kasa.

Labarai masu alaka