Me ya hana tsoffin shugabannin Najeriya zuwa rantsar da Buhari?

Bukola da Dogara sun halarci taron rantsarwa Hakkin mallakar hoto Sallau
Image caption Buhari na gaisawa da shugabannin majalisa masu barin gado

Abubuwan al'ajabi da dama sun faru a wurin bikin rantsar da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari a karo na biyu, da aka gudanar a dandalin Eagle Square.

Abu na farko shi ne yadda a wannan rana idan ka cire Yakubu Gowon, babu wani daga cikin tsofaffin shugabannin kasar da ke raye da ya halarci bikin rantsar da Shugaba Buharin.

Sai dai a irin wannan rana a 2015, kusan za a iya cewa dukkanin wani tsohon shugaban kasar ya halarci bikin da tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya mika mulki ga Muhammadu Buhari.

Masu sharhi kan al'amauran siyasa irin su Dr Tukur Abdulkadir na jami'ar jihar Kaduna sun danganta rashin halartar tsoffin shugabannin da abubuwa guda biyu:

  • Raba garin da Buhari ya yi da tsaffin shugabanni
  • Kokarin fifita ranar 12 ga watan Yuni

Dr Tukur ya ce "Ina tunanin tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ba zai halarci taron ba sakamakon yadda alaka tsakaninsa da Buhari ta yi har ta kai ana jifan juna da maganganu."

Dangane kuma da rashin zuwan tsohon shugaba Ibrahim Badamasi Babangida, Dr Tukur ya ce " Da alama rashin lafiyar da yake fama da ita ka iya zama dalilin rashin halartarsa."

Hakkin mallakar hoto Facebook/Nigeria Presidency
Image caption Tsohon Shugaba Yakubu Gowon lokacin rantsar da Buhari a Abuja

Shi kuwa tsohon shugaba Goodluck Jonathan "Zai wuya ya halarci bikin kasancewarsa jigo a jam'iyyar adawa ta PDP", in ji Dr Tukur Abdulkadir.

To amma Dr Tukur ya ce yana ganin "rashin halartar tsohon shugaba Abdussalam Abubakar ba ta da nasaba da bacin dangantaka da shugaba Buhari kasancewar shi Abdussalam din yana shiga kusan duk wata sabgar Buhari da aka gayyace shi. Illa dai kawai watakila ba a gayyace shi ba ne. Ana jira sai ranar 12 ga watan Yuni."

Wabi abu da ke kara fito da rashin jituwar shugaba Buhari da tsoffin shugabannin kasar shi ne yadda a wata hira ta musamman da shugaba Buhari ya yi da gidan talabijin na NTA kafin ranar rantsuwar, ya ce yana sane da cewa manyan kasar ba sa son sa kuma hakan ba ya damun sa ko kadan.

  • Latsa hoton da ke sama don kallon cikakkiyar tattaunawar.

Shugabannin duniya ba su je rantsuwa ba

Ba ya ga tsoffin shugabannin Najeriya, babu wani shugaban wata kasa da ya zo domin ya albarkaci taron bikin rantsuwa sabanin yadda aka saba a baya.

Bisa al'ada dai duk lokacin da za a rantsar da sabon shugaba musamman a kasashen Afirka, a kan gayyaci takwarorin aiki na kasashe ko da kuwa makwabta.

Hakkin mallakar hoto Sallau
Image caption Shugaba Buhari ya sha rantsuwar kama aiki

To sai dai Dr Tukur Abdulkadir yana ganin "Ba a gayyaci shugabannin duniyar ba ne ranar rantsuwar saboda irin gagarumin shirin da aka yi wa ranar 12 ga watan Yuni domin na ji an ce ma an gayyaci Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu."

Hakan a ta bakin Dr Tukur wani yunkuri ne na maye gurbin ranar 29 ga watan Mayu da shugabannin baya suka assasa da ranar 12 ga Yuni.

Mece ce ranar 12 ga watan Yuni

A watan Yulin 2018 ne dai shugaba Muhammadu Buhari ya amince da kasancewar ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimouradiyyar kasar a gwamnatance maimakon ranar 29 ga watan Mayu.

Shugaba Buhari ya ce ya yi hakan ne da manufar bai wa marigayi MKO Abiola don gwagwarmayar dawo da mulkin dimokradiyya a kasar, babbar lambar girmamawa ta GCFR a ranar bikin tuna wa da ranar zaben 12 ga watan Yunin shekarar 1993.

Hakan ya janyo suka da yabo daga 'yan kasar.

Jam'iyyar adawa ta PDP ta ce "akwai baki-biyu a matakin da shugaban ya dauka, domin ya yi aiki da gwamantin da Abiola ya mutu a hannunta."

To sai dai Dr Tukur Abdulkadir ya danganta batun na 12 ga watan Yuni da abubuwa guda biyu:

  • Buhari ya so kyautata wa kudu maso yamma domin neman tazarce
  • Buhari ya yi kokarin nuna shi mai gaskiya ne ta hanyar fito da "irin ingancin da nagartar mutane da zaben 12 ga watan Yuni" a idanun duniya.

Yanzu dai abun jira a gani shi ne ko za a ga tsoffin shugabannin kasar sun halarci bikin ranar 12 ga watan Yuni da za a yi makwanni biyu masu zuwa.