Yadda aka yi garkuwa da Najeriya da shugabanta

Masu garkuwa da mutane Hakkin mallakar hoto NIGERIA POLICE FORCE

Duk irin shagulgulan da za a yi a bikin rantsar da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari karo na biyu ba za su hana bayyanar irin kalubalen da yake gaban shugaban ba a sabon wa'adinsa, musamman na satar mutane don neman kudin fansa.

Hatta daya daga cikin 'yan uwan shugaban, Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar, bai tsira ba, domin kuwa yanzu haka yana hannun masu garkuwa da mutane bayan sun dauke shi a kofar gidansa a farkon wannan watan.

A jihar Kano ma an sace wani shahararren malami, wanda ya yi wa shugaban yakin neman zabe.

An yi garkuwa da shi ne a jihar Katsina kuma ya kwashe kwana 12 a hannun masu satar mutane domin karbar kudin fansa.

Hakkin mallakar hoto NIGERIAN ARMY

"Matasa takwas ne ke gadinmu, su sha sigari da wiwi kuma su hura mana hayakin. Su zage mu, su yi mana barazanar kisa tun da 'yan uwanmu basu kawo kudin fansarmu da wuri ba. Sun yi mana barazana iri-iri," in ji Sheikh Ahmed Sulaiman, a hirar da ya yi da jaridar Daily Trust.

Ya kara da cewa an sake shi ne ta hanyar musaya.

Gungun masu garkuwa kan sace masu kudi da talaka, inda sukan nemi kudin fansa har N30m, a wasu lokuta kuma su halaka wanda 'yan uwansa suka gaza biyan kudin fansar.

Gabannin fara gasar cin Kofin Duniya a bara, an sace mahaifin kaftin din Super Eagles Mikel Obi a karo na biyu, a wannan karon kuma an yi barazanar kashe shi.

"Na yi tsammanin bayan wasannin zan ji an ce sun kashe shi," in ji Mikel.

Ya ce sai da ya biya dala 28,000 (kimanin naira miliyan 10) kafin a sake shi.

Babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna ta yi kaurin suna wajen satar mutane, inda ake sace matafiya, dalilin da ya tilasta wa da dama daga cikinsu suke hawa jirgin kasa duk da cewa jirgin Kaduna yake tsayawa, akwai kuma matsalar tsada da karancin tikiti.

A watan Afrilun da ya gabata an yi garkuwa da wani babban dan siyasa na jam'iyyar APC da 'yarsa sannan aka kashe direbansa.

Wasu 'yan uwansa sun shaida wa BBC cewa an biya kudin fansa kafin a sake shi.

'Fuskantar karancin abinci'

Hakkin mallakar hoto AFP

An soma satar mutane domin karbar kudin fansa ne a yankin Niger Delta shekara 15 da suka gabata inda ake satar ma'aikatan kamfanonin man fetur, sai dai yanzu wannan sana'a ta game kasa baki daya.

'Yan bindigar sukan kwakwayi irin abubuwan da mayakan Boko Haram ke yi, inda suke shiga kauyuka a kan babura kuma su yi awon-gaba da mutane.

Lokacin da Buhari ya sha rantsuwar kama aiki a 2015, ya yi alkawarin kawo karshen Boko Haram, wadda ta daidaita rayuwar daruruwan mutane a yankin arewa masu gabashin kasar.

An rage wa 'yan bindigar karfi a baya-bayannan amma har yanzu suna kai hare-hare.

Mutane da dama na tsare a hannun 'yan kungiyar har da 'yan mata 100 da suka sace a garin Chibok a shekarar 2014.

Yanzu da yake tabarbarewar tsaro ta yi kamari, musamman a yankin arewa maso yamma, mutane na kara shiga cikin firgici.

Gwamnan jihar Katsina, wadda ita ce mahaifar Shugaba Buhari, ya shaida wa BBC cewa akwai yiwuwar fuskantar karancin abinci saboda tsoro yana hana mutane zuwa gonakinsu domin yin shuka.

Kalubalen da ke gaban Shugaba Buhari

Hakkin mallakar hoto AFP

Rashin tsaro: yaduwar sace mutane don neman kudin fansa musamman a yankin arewa maso yamma hadi da hare-haren bangaren Boko Haram da ke da alaka da kungiyar IS, su ne manyan abubuwan da za su fi daga masa hankali.

Tattalin arziki: Samun kashi 70 cikin 100 na kudin shiga daga man fetur da kuma hauhawar kayan masarufi na daga cikin abubuwan da ke kassara kasar.

Bankin duniya ya yi hasashen tattalin arzikin kasar zai karu da kashi 2.2 cikin 100 - wannan abari ne mara dadin ji domin kuwa rashin aikin yi a kasar ya kai kashi 20 cikin 100, inda kusan 'yan kasa ke cikin matsanancin talauci.

Cin hanci: Shugaban ya yi kokafi a wa'adinsa na farko wajen dakile cin hanci, wanda ya shi ne dalilin zurarewar biliyoyi daga baitulmalin gwamnati.

Sai dai an yi ta sukarsa bisa gazawa wajen daukar mataki kan wasu daga cikin na kusa da shi.

Aikin raya kasa: Duk da irin biliyoyi da aka zuba kan ayyukan raya kasa hukumar da ke kula da hannayen jari wato Securities and Exchange Commission ta yi hasashen cewa Najeriya za ta bukaci dala biliyan 878 nan da 2040 a matsayin kudaden cike gibi kan ayyukan raya kasa.

Hakan zai kawo mummunan nakasu ga ci gaban sana'o'i da 'yan kasuwa.

A watan jiya, majalisar dattawa Najeriya ta ce 'yan kasar da 'yan kasashen waje fiye da 4,000 ne ke ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa da mutane.

Ko da yake da dama daga cikin 'yan majalisar na ganin wannan adadin hasashe ne, suna masu cewa alkaluman za su iya wuce haka.

Babban Sufeton 'yan sandan kasar Mohammed Adamu ya ce tsakanin watan Janairu zuwa Afrilun bana, an sace kimanin mutum 685 kuma 365 daga cikinsu an sace su ne a yankin arewa-maso-yammacin kasar.

Yunkurin yaki da matsalar

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan kasar, Frank Mba, ya shaida wa BBC cewa ana sanya ido kan wasu jami'ansu wadanda ake zargi da hannu a satar mutane don neman kudin fansar.

Sai dai ya ce babu kwararan hujjoji da suka nuna cewa jami'an nasu na da hannu a satar mutane.

Ya ce matsalar satar mutane ta ragu bayan kaddamar da wani gagarumin aikin farautar masu garkuwa da jama'a wanda aka yi wa lakabi Operation Puff Adder.

Har ila yau ya ce an kama mutum 93 da ake zargi da satar mutane a mako biyu da suka wuce.

Shafin Twitter na rundunar 'yan sanda cike yake da labarai na yadda rundunar take kokarin dakile matsalar.

Sai dai akasarin 'yan Najeriya na da ra'ayin cewa har yanzu gwamnati bata tashi tsaye ba wajen magance wannan gagarumar matsala.

Hakan na faruwa ne a yayin da ake ci gaba da samun labaran yin garkuwa da mutane kusan a kullum, kamar yadda wani kanun labari kafar yada labarai ta Premium Times yake cewa: "An sace 'yan Najeriya 27 a jihohi hudu a sa'o'i 48".

Kazalika wasu kalaman da Shugaba Buhari ya yi game da babban sufeton 'yan sandan kasar lokacin da ya dawo gida daga ziyarar da ya kai London sun jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta.

"Ina ganin [babban sufeton 'yan sanda] yana ramewa ne saboda yana aiki tukuru," in ji Shugaba Buhari.

"Wannan yana nuna cewa shugaban nan bai dauke mu a bakin komai ba," in ji wani mai amfani da shafin Twitter.

Wani mai sharhi kan harkokin tsaro daga cibiyar nazari kan rikice-rikice ta International Crisis Group, Mr Nnamdi Obasi, ya dora alhakin tabarbarewar al'amuran ga rashin shugabanci nagari.

"Matsalar rashin aikin yi ta sa wasu matasa shiga aikata miyagun ayyuka," in ji shi.

Ya kuma ce yankunan karkara ne abin zai fi shafa.

"Akwai matsala a fannin tsaro kuma ba a hukunta wadanda aka samu da aikata laifi."

"Kazalika akwai matsalar cin hanci da rashawa tsakanin 'yan siyasa wanda hakan yake kawo ci baya ga al'umma," in ji shi.

Mr Obasi ya ce dole ne gwamnati ta samar da ayyukan yi sannan ta inganta rayuwar 'yan kasar idan ana so a kawar da matsalar garkuwa da mutane.

Bayani kan Shugaba Muhammadu Buhari a takaice:

  • Shekararsa 76
  • An zabe shi a matsayin shugaban kasa a ranar 28 ga Maris 2015
  • Ya yi shugaban mulkin sojan Najeriya daga 1984 zuwa 1985
  • An hambare shi a juyin mulki
  • An yi amanna ba ya cin hanci da rashawa
  • Mai ladabtarwa ne - a kan sa ma'aikatan gwamnati tsallen kwado idan suka makara zuwa aiki
  • Musulmi ne daga arewacin Najeriya
  • Ya tsallake rijiya da baya a wani hari da Boko Haram ta kai masa.