Kun san telan shugabannin Nijar?

Abubakar Sulaiman
Image caption Telan ya ce shi ya rika dinka wa shugaba Tandja Mamadou kaya a zamanin mulkinsa

Ba kasafai aka fiya sanin telolin mutanen da ke rike da manyan mukamai ba, BBC ta tattauna da telan da ya shafe shekaru yana yi wa shugabannin kasar Nijar dinki.

Alhadji Abubakar Sulaiman Tchiroma wanda ake kira Abba Tchiroma mazaunin birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, ya shafe sama da shekara 50 yana dinki ga shugabannin kasar da ministoci da manyan masu fada-a-ji.

"Tun daga kan shugaban kasa zuwa ministoci da ma sauran mutanen gari, babu wanda ban yi wa dinki ba," a cewar Abubakar Sulaiman, wanda yanzu girma ya cim masa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tandja Mamadou ya yi shugaban kasar Nijar daga 1999 zuwa 2010

Ya shaida wa BBC cewa daga cikin shugabannin da ya yi wa dinkin, babu wanda ya fi yi wa dinki kamar Tandja Mamadou, sai kuma Mamman Usman da dai sauransu.

Abubakar Tchiroma, ya ce shugaban kasar daya ne kawai bai yi wa dinki ba wato Mahammadou Issoufou shugaba mai-ci.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mahamadou Issoufou ya zama shugaban kasa a 2011

Telan ya ce ba wani abu ne ya sa ya samu nasara a wannan sana'a tasa ba illa cika alkawari.

Ya ce ' Cika alkawarina ne ya sa manyan mutane ke kawo mani dinki, domin idan aka kawo mani dinki na ce ga lokacin da za a zo a karba, to bana saba alkawari'.

Telan ya ce wasu manyan mutanen labarinsa ma suke ji a kan cika alkawarin, shi ya sa ma suke garzayawa suna kawo masa dinkin.

Abba Tchiroma, ya ce "A tsawon shekarun da na shafe ina dinki, bana jin akwai wanda na taba sabawa alkawari gaskiya".

Bayani a kan Halayyar teloli

A mafi akasarin lokuta teloli kan saba alkawari, wannan kuwa wata halayya ce da aka san su da ita.

Wannan dalili ne ya sa mutane kan canja teloli akai-akai saboda rashin cika alkawarinsu.

Da wuya ka ga wani ko wata ta rike tela guda, dole sai ka ga mutum guda na da teloli daga biyu zuwa sama.

A irin wannan halayya ta teloli ta rashin cika alkawari, a wasu lokuta har rigima kan kaure tsakanin tela da kwastoma, wani lokacin sai an kai ga hukuma wato 'yan sanda.