Sabbin gwamnoni na yin wurgi da tsarin da suka tarar

Facebook/Nigeria Presidency Hakkin mallakar hoto Facebook/Nigeria Presidency

Gwamnonin Najeriya da dama ne suka yi rantsuwar kama aiki a ranar Laraba, wasunsu a wa'adin farko wasu kuma a wa'adi na biyu.

Ba kamar Shugaban kasa Buhari ba wanda bai yi jawabin komai ba yayin bikin rantsuwarsa a dandalin Eagle Square da ke Abuja, duka gwamnonin da aka rantsar sun gabatar da jawabai bayan rantsuwar ta kama aiki.

Gwamnonin sun yi alkawura da dama, kuma akwai wasu abubuwa da suka ja hankalin jama'a da kafofin watsa labaran kasar a jawaban da gwamnoni suka yi.

Da yake Hausawa na cewa kowane allazi da na sa amanu, kowane gwamna abin da ya fi mayar da hankali ya sha bamban da abin da wani ya fi sakawa a gaba.

Dokar ta baci kan ilimi

Hakkin mallakar hoto Abdullahi Bego

Gwamnan Jihar Yobe wanda ya kama wa'adinsa na farko a ranar Laraba, Malam Mai Mala Buni ya ayyana dokar ta baci a bangaren ilimi.

A yayin jawabinsa bayan rantsar da shi, Mai Mala Buni na jami'iyyar APC ya ce za a gina karin makarantun firamare da na sakandare a jihar, za kuma a dauki karin malamai da kuma samar da karin kayan koyo da koyarwa.

Ya ce yana sane da yadda ake kara samun kwararar mutane a wasu yankunan, da kuma yadda wadanda rikin Boko Haram ya raba da muhallansu suke sake matsugunnai.

Gwamnan na Yobe ya kara da cewa, daukar matakin zai sa jihar ta sauya matsayinta daga wacce ke cikin wadanda suke koma baya a bangaren ilimi zuwa 'yan gaba-gaba a ci gaban ilimi.

Wani bangaren da dokar ta bacin za ta mayar da hankali a kai a cewar gwamnan shi ne bayar da kason jihar ga hukumar bada ilimin bai daya, domin baiwa jihar damar samun kason da ya kamata don inganta harkar ilimi.

Ilimi kyauta ga nakasassu da 'ya'yansu

Hakkin mallakar hoto Salihu Tanko Yakasai

Shi kuwa Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano alwakwarin baiwa nakasassu da 'ya'yansu ilimi kyauta ya yi a jihar tun daga firamare har matakin gaba da sakandare.

Ganduje wanda ya yi rantsuwar kama mulki a wa'adi na biyu ya ce ya dauki matakin ne da nufin karfafawa nakasassun gwiwa domin dogaro da kai.

Rushe nade-naden tsohuwar gwamnati

Hakkin mallakar hoto Inuwa Yahaya

A jawabinsa na kama aiki a matsayin gwamnan jihar Gombe Alhaji Inuwa Yahaya, ya sanar da rushe duk wasu nade-nade da gwanatin da ta gabace shi ta yi bayan zaben gwamna da aka yi a watan Maris din bana.

Haka kuma gwamnan ya sanar da soke rabon filayen da tsohuwar gwamnatin PDP ta yi gabanin ta bar mulki.

Gwamna Inuwa Yahya na jam'iyyar APC wanda ya fara wa'adinsa na farko a ranar Laraba ya kuma dakatar da daukar ma'aikatan da aka yi na sabuwar jami'ar jihar, wadanda aka yi gabanin rantsar da shi.

Sannan ya kuma soke duk kwangilolin da tsohuwar Gwmanatin ta bayar a baya-bayannan.

Haka kuma ya ce za a hukunta wadanda aka yi wa gwanjon kadarorin gwamnati a dai dai lokacin da yake shirin karbar mulki.

Kula da lafiya kyauta ga mata da yara

Shi kuwa sabon gwamnan Zamfara a arewa maso yamma Bello Matawalle ya bayyana cewa za a kula da lafiyar mata da yara kyauta a jihar.

Ya ce mata da yara a jihar ta Zamfara sun jima sun shan ukuba, amma yanzu lokaci ya yi da za a inganta rayuwarsu.

Gwamna Bello Matawalle ya ce gwamnatinsa za ta fara warware matsalar tsaro, ta yadda kowa zai yi rayuwarsa ba tare da fargaba ba.

Manyan ayyuka a kwana 100 na farko

A jihar Nasarawa da ke arewa maso tsakiyar Najeriya, Injiniya Abdullahi Sule aka rantsar a matsayin sabon gwamnan jihar wanda ya gaji Umaru Tanko Almakura.

A lokacin da yake jawabin kama aiki bayan rantsuwa, gwamnan ya zayyana wasu abubuwa 14 da ya ce zai yi kokarin cimmawa a cikin kwanakinsa 100 na farko.

Daga cikin abubuwan akwai yin garan bawul kan fansho da garatututi da kuma fara biyan kudin ga wadanda suka cancanta, da kuma yin duba kan kudaden albashi da ma'aikata ke bin gwamnati, sannan a fara biya.

Wani aikin kuma shi ne a cewar gwamna A A Sule shi ne kammala aikin filin jirgin sama na daukar kaya a birnin Lafiya.

Zan dauki matakai masu zafi, ku gafarta min tun yanzu

Hakkin mallakar hoto Kaduna Governor on Twitter
Image caption Gwamnan na Kaduna ya ce zai ci gaba da yin ayykan da za su inganta rayuwar 'yan Kaduna

Malam Nasi El-rufai na daga gwamnonin da suka kama rantsuwar aikin wa'adi na biyu, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da daukar matakai masu zafi da ba za su yi wa wasu dadi ba, don haka ya ce tun yanzu yana so jama'a su yi masa afuwa.

A jawabinsa na kama aiki karo na biyu, El-rufai ya ce ya ga ribar jajircewa da yin aiki don al'umma ko da kuwa matakan da ya dauka ba su yi wa wasu dadi ba.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa daga yanzu mata ma'aikata da suka haihu za su rinka yin hutun wata shida, ta yadda 'ya'yansu za su yi wayo kafin su koma zuwa aiki.

Akwai wadanda ba sa son ganin Legas ya sauya

Image caption Babajide Sanwo-Olu ya yi shirin tunkarar kalubalen Legas

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, jim kadan bayan rantsar da shi a dandalin taro na Tafawa Balewa Square da ke birnin na Legas, ya yi shagube ga 'yan siyasar da ya bayyana da "Yan bakin ciki' da ya ce ba sa son ci gaban birnin.

To amma ya yi musu albishir cewa su jira su yi kallo domin yana da shiri na musamman kan birnin, inda ya ce zai dora kan abin wanda ya gada ya bari.

Mista Sanwo-Olu ya kuma ce "Kalubale na tunkarar mu kuma ya kamata mu yi shirin fuskantar sa".

Sai dai ya bayar da tabbacin yin aiki tare da mataimakiyarsa, Obafemi Hamzat domin cika alkawurran da ya dauka a fannin lafiya da ilimi da sufuri da kuma muhalli.

Zan gina gadojin sama uku a Port Harcourt

Image caption Governor Nyeson Wike lokacin da ya sha rantsuwa

Gwamna Nyeson Wike na jihar Rivers wanda ya sha rantsuwar kama aiki wa'adi na biyu ya ce 'za mu mayar da hankali kan gina birnin Port Harcourt da samar da tsaro da kuma tsaftar muhalli'.