'Yan awaren Kamaru sun ba da sharuddan tattaunawa

Sisseku Ayuk Tabe, l Ayananen shugaban kasa Jamhuriyar Amazonia Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sisseku Ayuk Tabe, Shugaban 'yan awaren Amazonia

Sisseku Ayuk Tabe, wanda ya ayyana kansa a matsayin shugaban 'yan awaren Amazonia ya zayyano cikin wata wasika da ya rubuta daga dakinsa na gidan yarin da ake tsare da shi.

Ya ce sharuddan idan ba su hadu ba, ba zai amince ya tattauna da gwamnatin kasar ta Kamaru ba.

Ya kuma bukaci tsagaita wuta a baki daya cikin yankunan Arewa maso yammaci da kudu maso ammaci, sannan kuma a saki daukacin mutanen da ake tsare da su tun farkon tawayen a yankunan Inglishin kasar.

Har ila yau ya bayyana cewa tattaunawar ba za ta yiwu ba har sai in domin a duba yadda za a ba yankunan Inglishin biyu 'yancin kansu ne.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ba za a tattauna kan batun 'yancin kan 'yankunan Inglishi ba in ji Ministan harkokin wajen kasar Kamaru, Lejeune Mbella Mbella

Hukumomin gwamnatin kasar nada ra'ayin cewa ba za a tattauna kan batun 'yancin kan yankunan Inglishi ba, ra'ayin da ministan harkokin wajen Kamaru Lejeune Mbella Mbella ya jadadda a wannan makon.

Wannan kuma ba shi ne kadai batun da aka kasa cimma matsaya akai ba, saboda 'yan awaren na son a gudanar da tattaunawar ne karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya a wata kasa ta waje.

Sai dai matakin da kawo yanzu bai gamsar da hukumomin gwamnati ba.

A cewar Lejeune Mbella Mbella ya zama wajibi a yi wannan tattaunawa a Kamaru.

Gwamnati na son zama kaifi daya kan wannan batu: Za a magance wannan matsala ba tare da kasashen ketare sun tsoma bakinsu ba.

Matsalar ta barke ne bayan wani yajin aiki a shekarar 2016.

Sai rikice-rikice suka biyo baya abin da ya haddasa mutuwa fiye da mutane 2,000, in ji hukumomin Majalisar Dinkin Duniya.

Hukumomin na Majalisar Dinkin Duniya, sun kiyasta sama da mutane 'yan Kamaru rabin miliyan ne wannan rikici ya tilasta wa barin muhalansu, inda suka yi hijira a wasu bangarori na kasar ko ma kasashen waje.

Sai dai gwamnati ba ta amince da wannan kiyasi na rikicin yankunan Inglishi da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya suka bayar ba.

Kamaru kasa ce mai amfanin da Turanci iri biyu, sai dai wasu mazauna yankunan Inglishi na zargin cewa gwamnatin kasar ta ware su.

Labarai masu alaka