Kun san telan shugabannin Nijar?

Tandja Mamadou Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Telan ya ce shi ya ringa dinkawa shugaba Tandja Mamadou kaya a zamanin mulkinsa

Ba kasafai aka fiya sanin telolin mutanen da ke rike da manyan mukamai dinki ba, to amma BBC ta neme telan da ya shafe shekaru yana yi wa shugabannin kasar Nijar dinki. Kun san sirrinsa sa?

Alhadji Abubakar Sulaiman wanda ake kira Abba Tchiroma mazaunin birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar, ya shafe sama da shekara 50 ya nadinki ga shugabannin kasar da ministoci da manyan masu fada a ji.

"Tun daga kan shugaban kasa zuwa ministoci da ma sauran mutanen gari, ba wanda ba ya yi wa dinki ba," a cewar Abba Tchiroma, wanda yanzu girma ya cimma sa.

Ya shaidaw BBC cewa daga cikin shugabannin da ya yi wa dinkin, ba wanda ya fi yi wa dinki kamar Tandja Mamadou, sai kuma Mamman Usman da dai sauransu.

Abba Tchiroma, ya ce shugaban kasar daya ne kawai bai yi wa dinki ba wato Mahammadou Issoufou mai ci yanzu.

Telan ya ce ba wani abu ba ne ya sa ya samu nasara a wannan sana'a ta sa ba illa cika alkawari.

Ya ce ' Cika alkawarina na ne ya sa manyan mutane ke kawo mini dinki, domin idan aka kawo mini dinki na ce ga lokacin da za a zo a karba, to bana saba alkawari'.

Telan ya ce wasu manyan mutanen labarinsa ma suke ji a kan cika alkawarin, shi ya sa ma suke garzayawa suna kawo masa dinkin.

Abba Tchiroma, ya ce "A tsawon shekarun da na shafe ina dinki, bana jin akwai wanda na taba sabawa alkawari gaskiya".

Bayani a kan Halayyar teloli

A mafi akasarin lokuta teloli kan saba alkawari, wannan kuwa wata halayyace da aka sansu da ita.

Wannan dalili ne ya sa mutane kan canja teloli akai-akai saboda rashin cika alkawarinsu.

Da wuya kaga wani ko wata ta rike tela guda, dole sai ka ga mutum guda na da teloli daga biyu zuwa sama.

A irin wannan halayya ta teloli ta rashin cika alkawari, a wasu lokuta har rigima kan kaure tsakanin tela da kwastoma, wani lokacin sai an kai ga hukuma wato 'yan sanda.

Hakkin mallakar hoto Getty Images