An tsige sarakunan gargajiya shida a Chadi

Idriss Deby Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gwamnatin Idriss Deby ta sallami sarakunan gargajiya

An kori sarakunan ne a cikin wata takarda da ministan harakokin cikin gida da kula da kananan hukumomi ya sanya wa hannu.

A takarda ta farko Minista Mahamat Abali Salah ya kawo karshen ayyukan wasu sarakunan gargajiya na gabashin kasar, inda a takarda ta biyu ne kuma aka dakatar da Sarkin Ouadai.

Wadannan matakai na dakatarwa sun biyo bayan wasu rigingimu da suka faru tsakanin wasu kabilu na kasar, da suka yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 40.

Wadannan rigingimu sun faru ne a yankunan Ouaddaï da Sila, a Gasbashi da kuma kudu maso gabashin kasar ta Chadi.

Ana zargin sarakunan da aka tube da nuna rashin ladabi da halin ko-in-kula kan abin da ya faru.

Minista Mahamat Abali Salah wanda shi ne ya sa hannu kan wannan hukunci, ya ce ana kuma ci gaba da gano masu hannu a bangaren gwamnati da ma bangaren jami'an tsaron Ouaddaï da Sila.

Abali Salah, ya kara da cewa sun gano sarakunan da aka tube daga mukamansu ba sa wani kokari dan magance rigingimu a yankunansu.

Labarai masu alaka

Karin bayani