Aisha ta nema ta yi fice a wasan kwallon doki
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Aisha Suleiman: Musulmar da ke kwallon doki a Kaduna

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon

A Najeriya musamman arewacin kasar, sabon abu ne a ga mace na buga wasan kwallon doki.

Amma Aisha Ahmad Suleiman, mai shekara 18 na neman yin fice a wasan kwallon doki.

Budurwar ta bayyana cewa ta fara da sha'awar dabbobi musamman dawakai wanda daga baya ta fara wasan kwallon doki.

Ta kuma ce ta fuskanci kalubale daban-daban bayan ta fara wasan kwallon dawaki.

Hada bidiyo: Fatima Othman

Labarai masu alaka