An yi awon gaba da mutum 13 a Nijar

Boko Haram Hakkin mallakar hoto AFP

Rahotanni daga yankin jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar da ke makwabtaka da jihar Borno da Kuma jihar Yobe a Najeriya, sun tabbatar da cewa wasu da ake zaton 'yan Boko Haram ne, sun yi awon gaba da wasu mutum 13.

Wannan lamari dai ya faru ne a garin Timur wanda ke da nisan kilomita 60 daga garin Diffa.

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa, a daren Laraba ne wasu da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne suka shiga garin na Timur inda suka yi awon gaba da mutane 13.

Ganau ya ce, daga cikin mutanen da aka sacen akwai matan aure uku da kuma wani malami wanda aka kashe.

Mutumin ya ce, har yanzu ba su san inda mutanen da aka sacen suke ba.

Ganau din ya ce, ' A gaskiya muna cikin halin zaman dar-dar a yankinmu, domin kuwa idan ka kwanta baka da tabbas a kan ko zaka tashi ko ba zaka tashi ba.'

Ya ce duk da jmi'an tsaro na iya bakin bakin kokarinsu, gaskiya akwai matsalar tsaro a yankinsu.

Mahukunta a kasar dai ba su ce komai ba a game da sace mutanen.

Ana dai yawan samun kai hare-hare a wasu yankuna na Jamhuriyar Nijar, wanda kuma ya ke sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama.

Ko a kwanakin baya ma kungiyar IS mai da'awar kafa daular musulunci ta yi ikirarin daukar alhakin mummunan harin da ya yi sanadin mutuwar a kalla sojojin Nijar 29 a kusa da kan iyakar Mali.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar 16 ga watan Mayu, IS ta ce mayakanta sun far wa ayarin motocin sojojin Nijar a Tongo Tongo ranar 14 ga watan Mayu, sannan 40 daga cikin sojojin ne suka mutu ko suka jikkata.

Mayakan sun yi kwanton bauna ne a wani yanki inda aka taba kashe sojojin Amurka hudu a watan Oktoban 2017, yayin da suke wani atisaye na hadin gwiwa tsakanin dakarun Nijar da dakarun Amurka na musamman, inda a wancan lokacin ma mayakan IS suka far musu.

Labarai masu alaka