'Yan Najeriya na kokawa kan matsalar wutar lantarki'

Ana matsalar wutar lantarki a Najeriya Hakkin mallakar hoto DailyDigest Nigeria

Al'ummar Najeriya na ci gaba da kokawa kan rashin wutar lantarki, wadda hakan ke kara haddasa matsin tattalin arziki.

'Yan kasar na kokawa ne a yayin da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya fara wa`adin mulki karo na biyu,

Duk da kasancewar Najeriya babbar kasa mai arzikin ma'adanin kwal da man fetur da iskar gas, sannan kuma wadda ta fi kowacce fitar da danyan fetur a nahiyar Afirka, rahotannin sun nuna kashi 40 cikin 100 na al'ummar kasar ne kadai ke samun wutar lantarki.

Rashin wutar lantarki dai na janyo matsaloli da dama musamman wajen tafiyar da abubuwa da suka hadar da kasuwanci da bangaren aikin gona da masana'antu da asibitoci da makarantu da dai sauransu.

Wani da ke aiki a gamayyar kungiyoyin da ke sa ido kan yadda ake rarraba wutar lantarki a jihar Kano da ke arewacin Najeriyar, Malam Nasiru Kura, ya shaida wa BBC cewa, samar da wutar lantarki a Najeriya na tare da matsaloli.

Ya ce tun farko ma ba a bi layin da ya kamata abi ba, saboda a Najeriya akwai wasu bangarorin da ke da rana da hamada, to ba a yi amfani da hasken ranar ba wajen samar da wutar.

Malam Nasiru Kura, ya ce dangane da amfani da iskar gas wajen samar hasken lantarkin, har yanzu ana samun jayayya tsakanin kamfanin mai na kasa wato NNPC da kuma NIPP.

Ya ce a yanayin da ake ciki a kasar bisa la'akari da yawan jama'a, to ya kamata a ce an samu hanyoyin samar da wutar lantarki da dama, ma'ana a hada da na hasken rana da ta gas da kuma ruwa.

Ya ce, idan har aka yi amfani da wadannan hanyoyin to ko shakka ba bu za a samu wadatacciyar wutar lantarki a kasa, kuma tattalin arzikin kasar ma zai kara habaka.

Karin bayani

Rashin wadatacciyar wutar lantarki a Najeriya, abu ne da ke ci wa al'ummar kasar tuwo a kwarya musamman wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum.

Masu sana'oi da dama da ke bukatar wutar lantarkin a koda yaushe na cikin amfani da janarreto wanda hakan kuma ke sa al'amuransu komawa baya.

Haka a ma'aikatu ko asibitoci ma, a kodayaushe sai dai kaga ana amfani da inji.

Labarai masu alaka