'Yadda bashi ya yi wa wasu jihohin Najeriya katutu'

Gwamnonin jihohin Najeriya Hakkin mallakar hoto Presidency

Sakamakon wani bincike ya bayyana cewa Lagos ce jihar da ake bi bashi fiye da sauran jihohi 36 na Najeriya.

Binciken wanda wata mujallar tattalin arziki Economic Confidential ta wallafa ya yi bayani ne kan yawan bashin da ake bin jihohin Najeriya wanda suka ciyo a cikin gida da waje a 2018.

Rahoton ya ce yawan bashin da ake bin jihar Lagos ya kai kusan kashi 20 na jimillar basukan da jihohin 36 suka ci hadi da Abuja babban birnin Tarayya, wanda ya kasance tiriliyan N5.376 a 2018.

A cewar rahoton ana bin Lagos bashin cikin gida kudi Naira tiriliyan N1.043 a 2018, na waje kuma tiriliyan N513.514.

Sauran jihohin da ke sahun gaba da suka fi cin bashi sun hada da Edo da ake bi sama da biliyan N99 da Kaduna da ake bi sama da biliyan N81 sai Cross Rivers da ake bi sama da biliyan N67 da Bauchi da ake sama da biliyan N48.

Jihar Kaduna ce ta uku cikin jihohin da suka fi cin bashi, Kano kuma tana matsayi na 17 cikin jihohi 36.

Hakkin mallakar hoto Presidency
Image caption Zamfara tana matsayi na 30, Kogi kuma tana matsayi na 31 daga cikin jihohin da suka fi cin bashi

Jihohin arewa maso gabas ne da ke fama da barazanar Boko Haram, rahoton ya ce ba su ci bashi ba sosai inda Taraba ce ta farko da ba ta ci bashi sosai ba cikin jihohin Najeriya inda ake binta naira biliyan N7.780, sai jihar Borno da ake binta bashin naira biliyan 7.782, Yobe kuma ana bin ta bashin naira biliyan 9.895.

Daga cikin jihohi 36 na Najeriya, rahoton ya ce jihohi biyar da suka hada da Sokoto da Katsina da Yobe da Jigawa da Niger ne ba su ci bashi sosai a ciki da waje ba.

Rahoton na zuwa ne a yayin da jihohi da dama ke fama da matsalar rashin kudi musamman kudaden shiga na cikin gida, domin gudanar da ayyukan da suka shafi ci gaba da raya al'umma.

Yawancin jihohin sun dogara ne da kason kudaden da suke samu daga asusun tarayya.

Labarai masu alaka