Alfanun Zakkatul Fitr
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ko kun san alfanun bayar da zakkar fidda kai?

A yayin da al'ummar musulmi ke kammala azumin watan Ramadan, wani abu da ya wajaba musulmi mai hali ya yi shi ne fitar da zakkar fidda-kai.

Ita dai wannan zakka kamar yadda addinin musulunci ya yi tanadi, tana da matukar amfani musamman wajen taimaka wa wadanda ba su da abinda za su sa a baka a lokacin bikin sallah.

ZakkaR fidda kai dai sunnah ce daga cikin sunnonin Manzon Allah SAW.

Ana so ne a fitar da wannan zakkar kai kafin tafiya masallacin idi.

Ku saurari tattaunawar da BBC ta yi da Sheikh Tukur Almannar, malami a garin Kaduna da ke Najeriya kan zakkar ta fidda kai.

Karin wasu labaran

Za a daure duk wanda aka kama yana bara a Uganda

Mutane sun mutu bayan sun ci shinkafa a wajen bauta

Labarai masu alaka