Yau take Sallah a Najeriya

Getty Images Hakkin mallakar hoto Getty Images

A cikin bayanin da ya yi, mai alfarma Sarkin musulmi Sa'ad Abubakar ya ce Litinin 3, ga watan Yuni ce rana ta karshe ta azumin watan Ramadan na shekara 1440.

Ya ce an samu rahoton ganin wata daga sarakuna kamar Shehun Borno da Sarkin Gwandu da Sarkin Dutse da sarkin Jema'a da sarkin Machina da kuma sauran wasu sassa na Najeriya.

Sarkin musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar III ya ce ganin jinjirin watan da aka yi a garuruwa daban-daban na fadin kasar ya sanya Talata 4 ga watan Yuni, 2019 ta zamo 1 ga watan Shawwal, 1440.

Akasarin Musulmai a fadin duniya dai sun tashi da Azumin watan Ramadan ranar shida ga watan Mayun 2019.

Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa da safiyar Litinin din nan ne al'ummar musulmi a kasar Mali suka yi sallar Idi.

Hakan na nufin Litinin din ta zama daya ga watan Shawwal ke nan a kasar.

Al'ummar kasar ta Mali dai sun fara azumin watan Ramadan din ne ranar Lahadi ta hudu ga watan Mayu sabanin yadda akasarin kasashen musulmi a fadin duniya suka tashi da azumin ranar Litinin.

Haka ma a Najeriyar dai Mabiya mazhabar Shi'a karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Elzakzaky sun bayyana cewa ranar Litinin ce daya ga watan Shawwal bayan samun tabbacin ganin wata da yammacin Lahadi.

Labarai masu alaka