Amurka ta ba sojojin Nijar taimakon motoci

Wasu motoci da kasar Amurka ta ba sojojin Nijar
Image caption Wasu motoci da kasar Amurka ta ba sojojin Nijar

Dan taimakama sojojin kasar ta Nijar a yakin da suke da 'yan ta'ada ne, kasar Amurka ta ba sojojin da ke yaki cikin rundunar hadin gwiwa ta G5 Sahel karin kayan yaki.

Wadannan kaya sun hada da manyan motoci na shiga daji, da wasu na'urorin yaki na aiki a daji.

A hira da BBC ministan tsaron kasar ta Nijar Kalla Moutari ya bayyana cewa kayan da suka samu daga kasar ta Amurka kari ne kan abin da suka mallaka, inda ya maida martani kan masu cewa sojojin kasar ta Nijar ba su da isassun kayan aiki.

Image caption Wata na'ura da Amurka ta ba sojojin kasar Nijar

Ya ce batun ba haka yake ba hasali ma idan aka yi la'akari da yadda ga baki daya iyakokin kasar Nijar na fuskantar barazanar tsaro, amma kuma kasar take zaune lafiya.

Kasar Amurka ta bakin jami'in kula da hulda da jama'a a ofishin jakancin ta a Nijar Idi Baraou ya ce wannan bashi ne karo na farko ba.

Har ila yau ya ce ba zai kuma zama na karshe ba da kasar ta Amurka za ta ba da taimako ga sojojin kasar Nijar.

Kasar Nijar na fuskanta matsaloli a iyakokinta na kusurwowin hudu.

Image caption Wasu sojoji bayan da suka karbi taimako

Bayan matsalar hare-haren 'ya'yan kungiyar Boko Haram da ya ta gayyarar da jihar Diffa, jihohin Tahoua, Agadez, da kuma Tillabery na fuskantar matsalar masu ta da kayar bayan addini da ke kai hare-hare ta kusan ko'ina cikin wadannan jihohi.

Jihar Maradi mai iyaka da jihohin Sokoto da Zamfara na fuskanta matsalar sata mutane don neman kudin fansa.

Labarai masu alaka