Wasika ga Gwamna Ganduje kan Sarki Sanusi - Farfesa Jibril

Jibril Ibrahim Hakkin mallakar hoto Daily Nigerian
Image caption Farfesa Jibril Ibrahim

Farfesa Jibril Ibrahim wanda shi ma dan asalin jihar Kano ne ya rubuta budaddiyar wasika ga gwamnatin jihar Kano kan dambarwar da ke faruwa tsakaninta da masarautar Kano, a 'yan kwanakin nan.

Gidan jaridar Daily Trust ne suka wallafa wannan wasika a harshen turanci. Ga fassararta;

Na ga wasikar neman bahasi da aka aika wa Sarkin Kano, inda aka ba shi awa 48 ya yi bayani kan rahoton wucin gadi da hukumar yaki da rashawa da cin hanci da sauraron korafe-korafe ta jihar Kano ta yi.

Lafazi da abun da takardar ta kunsa na nuni da irin yadda ake son daukar matakin gaggawa a kan wannan rahoto. Hakan ne kuma ya sa ni rubuta wannan budaddiyar wasika.

Tun 8 ga watan Mayun 2019 ake zaman zulumi a Kano, lokacin da gwamnatinka ta fara daukar matakin karkasa masarautar Kano.

Wannan mataki yana da illa sosai ga al'ummar Kano. A saboda haka nake rokon ka bisa girmamawa da ka janye daga wannan lamari saboda dalilai kamar haka:

Na farko, Najeriya na fama da matsalolin tsaro a sassan kasar da dama kuma al'amarin ya sha kan jami'an tsaronmu. Kano ta kasance wani wuri da yanzu rikici zai iya barkewa to amma a 'yan shekarun nan an samu zaman lafiya.

A matsayinka na gwamna, yana da muhimmanci ka kasance jagora wajen tabbatar da ganin zaman lafiyar ya dore.

Hakan na nufin bai kamata ka yi abun da zai janyo rarrabuwar kai a tsakanin al'ummar jiharmu ba, kasancewar kana sane da irin rashin zaman lafiyar da datsa masarautar zai iya haifarwa.

Mai girma gwamna, ka tuna cewa a baya an samu irin wannan yanayin na karkasa masarautar.

Ranar 1 ga watan Afrilun 1981, a tsohuwar jihar Kano Gwamna Rimi ya kirkiri sabbin sarakuna guda hudu da suka hada da Auyo da Dutse da Gaya da kuma na Rano wadanda aka ce dai-dai suke da sarkin Kano.

Sannan kuma aka bai wa sarakunan Hadejia da Gumel da Kazaure martabar sarakunan yanka.

Gwamna Rimi ya kuma bayyana cewa sarakunan "ma'aikatan gwamnatin ne da ke karbar umarni daga hannun shugabannin kananan hukumominsu." A ranar 7 ga watan na Afrilun 1981 din, sakataren gwamnatin jihar ya aike wa da Sarki takardar neman bayani kamar haka:

"Gwamnan Kano, Alhaji Abubakar Rimi ya umarce ni na rubuta maka wannan wasika domin bayyana bacin ransa da na gwamnatinsa dangane da yadda kake mayar da martani ga gwamnati.

Al'umma na tsammanin za ka mutunta gwamnati kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Gwamnati ta fahimci cewa tun lokacin da gwamnatin nan ta hau karaga a 1971, akwai abubuwan da suke nuna rashin biyayya ga gwamnatin jihar Kano... saboda haka, gwamna ya umarce ni da na nemi ka kare kanka a cikin awa 48, sannan ka yi bayani kan dalilin da zai hana a dauki matakin ladabtarwa a kanka."

Bayan aikewa da wannan takardar ta neman bahasi, a ranar 10 ga watan Yulin 1981, 'yan daba suka kai hari kan wasu ma'aikatu da suke ganin na kare muradun gwamnati, inda suka kashe mutum 34 sannan suka kona ma'aikatu kamar gidan Rediyon Kano da gidan Jaridar Triumph.

'Yan dabar sun kuma kashe mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin siyasa, Dr Bala Muhammad wanda a lokacin ya ke rubuta takardar tsige sarkin.

Hare-haren 'yan dabar ya karu a birnin Kano duk da cewa ba a san ran mutane ba hakan ya faru.

Image caption Yadda aka raba masarautun Kano

Abu na biyu, masarautar Kano tana da kimar da bai kamata ta rushe a hannunka ba. Abun zai yi muni idan ka shiga tarihin wanda ya rusa masarautar Kano.

Ita wannan masarauta ta kafu ne tun 999AD, inda kuma ta koma karkashin daular Sokoto, bayan Jihadin da aka yi a 1804-1807.

Tun lokacin ne masarautar karkashin wanda ake kira Sarki, ta zama mafi karfin fada a ji a daular ta Sokoto, har kuma lokacin da ta zama jiha. Masarautar ta zama tumbin giwa inda ta kunshi mutane iri daban-daban daga fadin Najeriya da ma Afirka.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu shi ne sarkin Kano na 57, sarautar da take da tarihi kuma ita ce ta biyu bayan Sarkin Musulmi.

Sarautar ta addini ce, amma kuma tana da tasiri ga shugabannin siyasa sannan kuma tana taimaka wa wajen ganin an yi gaskiya da adalci a harkar gwamnati.

Bai kamata a ce mai girma gwamna ne zai rusa irin wannan abu mai girma ba.

Na uku, ya kamata ka janye daga daukar wani mataki domin ka girmama doka.

Idan za ka tuna a ranar 23 ga watan Mayu, mai shari'a Badamasi ya umurci gwamnati da ta dakata a kan daukar wani mataki wajen tabbatar da dokar sarakuna da majalisar jihar ta yi ko yin wani abun da zai taba mutuncin masu nada sarki ko sarkin kansa bayan an shigar da kara.

Akwai shari'a guda biyu da ke gaban kotuna a yanzu haka, bai kamata gwamna ya raina kotu ba.

A mahawarar da aka tafka a kotu, wasu sun nuna cewa akwai matsala sosai wacce ba za a iya magance ta ba ga mutanen Kano idan har ba a rushe abubuwan da suka faru a baya ba.

A zahiri, tunanin cewa majalisar jiha za ta iya kafa wasu masarautu rashin fahimta ne cewa ita kanta masarautar Kano doka ta kafa ta.

Babu wata doka da ta kafa masarauta wadda ta kafu a tarihi ko a matsayin al'adar mutanen Kano.

Matakin majalisar jiha na gaggauta tabbatar da dokar a cikin awa 48 ba tare da bai wa jama'a dama ba da kuma bijirewa umarnin kotu wajen tabbatar da sabbin sarakuna duk da sanin cewa lamarin na gaban kotu, kuskure ne kuma bai kamaci gwamna ba.

Kamar yadda lauyoyin masu nada sarki suka bayyana, a karkashin gyaran dokar, majalisa ta cire sashe na uku da ke da dangantaka da nada sarki, inda aka maye gurbin sashen da sabon sashe na uku da ke magana kan kirkirar majalisar sarakuna ta jiha, da kuma kirkirar saabbin masarautu.

Babu wani sashe a sabuwar dokar da ya ba wa gwamna ikon nada sababbin sarakuna ko ma ya tabbatar da zaben da masu zabar sarki suka yi.

Ko ma dai mene ne babu wata hujja da ke nuna cewa akwai masu zabar sarki a babbin masarautun, ko kuma ace sun taba haduwa domin zabar sarki ko kuma suka tura wa gwamna sunan wani domin amince wa.

Abin da ka yi bai da tushe a shariance, don haka ya kamata a warware matakin.

Daga karshe, zargin kashe kudin masarauta ba bisa ka'ida ba da ake yi wa sarki bai da wani tushe illa dai irinsa ne aka yi amfani da shi aka cire Sarki Sanusi na daya.

Kamar yadda ake cewa, mutanen da ke gidan gilashi za su iya jifa da duwatsu, to amma fa kaikayi zai iya komawa kan mashekiya. Mutanen Kano suna sane da hakikanin zargin rashawa kuma suna da bidiyo a kan hakan.

Mai Girma Gwamna, ina rokonka ka yi duban tsanaki kan wadannan batutuwa da muhimmanci, tare da fatan cewa hakan zai sa ka dauki matakin janyewa daga hanyar rusa masarautar Kano da kuma cire sarkinmu mai daraja.

Naka a kodayaushe

Jibrin Ibrahim.

Labarai masu alaka

Karin bayani