Kun san abubuwa hudu da za su faru a wannan makon?

Yau take Litinin wadda ke nuni da cewa mun shiga sabon mako. Duk da cewa ba mu san duka abubuwan da za su faru a wannan makon ba, amma akwai batutuwan da muke hasashen su ne za su iya faruwa a makon.

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da muke sa ran za su faru a makon.

1- Za a rantsar da Majlisar Tarayya a Najeriya

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ita ce majlisa ta tara da za a rantsar a Najeriya

A ranar Talata 11 ga watan Yuni ne sababbin 'yan Majalisar Tarayya a Najeriya za su sha rantsuwar kama aiki.

'Yan majalisar za su maye gurbin wadanda suka gabatar da aiki ne daga shekarar 2015 zuwa 2019, kuma ita ce majalisa ta tara.

Sanatoci 109 ne ake sa ran za a rantsar da kuma 'yan majalisar wakilai 360.

Har wa yau, a wannan rana ce kuma za su zabi shugabannin da za su jagoranci majalisun biyu.

2- Ranar Dimokradiyya a Najeriya

Hakkin mallakar hoto Facebook/Nigeria Presidency
Image caption Shugaba Buhari ya fara wa'adin mulkinsa na farko ne a shekarar 2015

Ranar 12 ga watan Yuni ita ce Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar 'Ranar Dimokradiyya' a Najeriya a madadin 29 ga watan Mayu.

Ranar Laraba mai zuwa ita ce ranar da za a fara gudanar da bikin bayan an samu canjin, inda ake sa ran za a yi shagulgulan bikin rantsar da gwamnatin Buharin a karo na biyu wanda ba a yi ba a ranar 29 ga Mayu.

3- Ranar Zabaya ta Duniya

13 ga watan Yuni ita ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar Zabaya ta Duniya.

A ranar 18 ga watan Dismabar 2014 ne majalisar ta ware wannan rana domin wayar da kan al'umma game da zabaya.

Hakkin mallakar hoto UN

4- Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar kwallon kafar mata ta Najeriya wato Super Falcons za su kara da takwarorinsu na South Korea a ci gaba da wasannin gasar cin Kofin Duniya ta mata da ake yi a kasar Faransa.

Za a buga wasan ranar 12 ga watan Yuni da misalin karfe 2:00 na rana agogon Najeriya da Nijar.

Najeriya ta sha kashi a hannun 'yan matan kasar Norway da ci 0-3 da nema a wasan farko ranar Asabar da ta gabata.

Labarai masu alaka