An kashe a kalla mutum 100 a Mali

Malian Army Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An dade ana samun hargitsi tsakanin kabilun Fulani da Dogons da ke tsakiyar kasar ta Mali

Wasu mutane dauke da makamai sun afka wa garin Dogon na kasar Mali, inda suka kashe kusan mutum 100.

An kai wannan hari ne a Sobane-Kou kusa da garin Sanga. Maharan sun kuma cinna wa gidaje wuta, inji shaidun gani da ido.

Wani zababbe na yankin ya shaida wa BBC cewa an gano gawarwakin mutane da suka kone kurmus, sanan ya ce ana ci gaba da bincike dan gano wasu karin gawarwakin.

An dade ana samun hargitsi tsakanin kabilun Fulani da Dogons a tsakiyar kasar ta Mali, inda kabilun biyu ke kai hare-haren ramuwar gayya.

Ko ranar 23 ga watan Maris da ya gabata akalla Fulani 160 ne wasu ma farauta Dogons suka kashe a Ogossagou, wani gari da ke kusa da iyaka da kasar Burkina Faso.

Baya ga fadace-fadacen kabilanci, yankin na fuskantar hare-haren masu tayar da kayar bayan addini tun 2012.

An sha zargin Fulani, wadanda akasarinsu musulmai ne da mara wa masu fafutukar addini baya.

Suna zargin gungun maharban Dogon da ake kira 'Dan Na Ambassagou' da kai masu hari. Gwamnatin kasar Mali ta rushe gungun na 'Dan Na Ambassagou' bayan harin da aka kai wa garin Ogossagou.

Labarai masu alaka