Annobar kyanda ta barke a jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo

Campagne de vaccination contre la rougeole Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jamhuriyar Dimokradiyar Kongo ta sanar da fara gangamin rigakafin yaki da cutar

Annoba cutar kyanda ta barke a jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo.

Ofishin ministan kiwon lafiyar kasar ne ya bayyana cewa an samu mutane 87,000 da ake zaton sun kamu da cutar tun farkon wannan shekara kawo yanzu.

An samu barkewar wannan cuta a yankuna 23 daga cikin 26 na kasar a birane da karkara.

Duk da cewa ana saukin kamuwa da cutar, ana iya kiyaye kamuwa da ita ta hanyar yin rigakafi.

Sai dai cutar na fuskantar kwan gaba kwan baya cikin kasar ta dalilin karancin ababen hawa, matsalar tsaro da ma yadda fannin na kiwon lafiya ke fuskanta karancin kayan aiki.

Bayan wadannan matsaloli, akwai batun rashin takamaiman tsarurukan rigakafi, ana samun gazawa ko kuma yankewar rigakafi, batun kula da magani saboda rashin kyawon wuraren ajiya masu sanyi.

Ana shirya yaki da wannan cuta ta hanyar tura lokitocin yankunan da taimakon kungiyoyin agaji kan fanin kiyon lafiya irin u Medecins Sans Frontieres.

Kungiyar ta ce tana yaki da yaduwa cutar kyanda, tare da hukumomin kiwon lafiya cikin yankuna 10 na kasar.

Yankuna kuma su ne Haut-Lomani, Lualaba, Tanganyika, arewacin-Kivu, kudancin-Kivu, Tshopo, Kasai, Kasai ta tsakiyal, Haut-Uele da kuma Ituri.

Kawo yanzu dai cutar ta yi ajalin fiye da mutum 1,500 a kasar daga farkon wannan shekara kawo yanzu. Mafi yawansu kuma yara ne 'yan kasa da skekara biyar da haihuwa.

Offishin ministan kiwon lafiya kasar ya ayyana barkewa annobar ne a ranar Litanin.

Wata majiya ta kusa da hukumomin kasar ta bayyana wa BBC cewa ana ci gaba da tattara kudaden da za su ba da dama shirya gangamin na rigakafi don kare yaduwa kwayoyin cutar cikin yankunan da cuta ba ta kai ba.

Sama da yara miliyan biyu ne suka samu rigakafin a watan Afrilun wannan shekarar, wasu karin miliyan 1.4 za su samu cikin 'yan kwanaki masu zuwa a yankunan da cutar ta riga ta bulla.

A cikin wata sanarwa kungiyar likitoci ta Medecins Sans Frontieres ta fitar ta yi gargadin cewa wannan annoba na iya zama mafi kisa tun bayan annobar da aka yi a kasar a tsakanin shekarun 2011 zuwa 2012.