Tarihin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan

Sanata Ahmed Lawan Hakkin mallakar hoto Senate
Image caption Ahmed Lawan ya shafe shekara 20 a majalisar tarayya

Kusan za a iya cewa burin Sanata Ahmed Ibrahim Lawan ya cika a siyasance bayan da aka zabe shi a matsayin shugaban majalisar dattawa ta Najeriya.

Ya kayar da Sanata Ali Ndume da tazarar kuri'a 51, inda ya samu kuri'u 79, shi kuma ya samu 28.

Nasarar tasa ta zo ne shekara hudu cir bayan da ya sha kaye a hannun Bukola Saraki a wani yanayi mai cike da rudani.

Sanata Ahmed Lawan, wanda ke wakiltar Arewacin Yobe, gogaggen dan majalisa ne wanda ya shafe shekara 20 a zauren majalisar tarayya.

An fara zabarsa ne zuwa majalisar tarayya a shekarar 1999, inda kuma ya kasance a can har zuwa shekarar 2007.

Ya shugabanci kwamitoci daban daban da suka hada da na ilimi da kuma ayyukan noma.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ali Ndume ya rungumi kaddara yayin da ya fadi zaben jagorancin majalisar dattawa

'Ya iya allonsa'

Dr Ahmed Lawan, wanda aka haifa a shekarar 1959 a jihar Yobe, inda kuma ya yi digiri na farko a jami'ar Maiduguri, kafin ya yi na biyu a Jami'ar Ahmadu Bello da kuma na uku a Burtaniya, ya zama Sanata a 2011.

Ya shugabanci kwamitoci daban daban, kuma ya zama mamba a kwamitin gyaran tsarin mulki na kasa.

An nada shi shugaban masu rinjaye bayan da aka sauke Sanata Ali Ndume a wani yanayi mai cike da rudani.

Sanata Lawan ya shafe shekaru yana siyasar ne a karkashin jam'iyyar ANPP, wacce daga bisani ta narke a hadakar jam'iyyun da suka kafa jam'iyyar APC mai mulki a yanzu.

Mutum ne wanda ya iya allonsa a siyasa domin kuwa sabanin yadda ake jin kan wasu 'yan majalisa da gwamnoninsu, Ahmed Lawan ya yi aiki da gwamnoni daban daban a Yobe, amma ya zauna lafiya da su.

Masu lura da al'amura na ganin hakan na daga cikin muhimman abubuwan da suka ba shi damar dadewa a majalisar tarayya.