Wane ne Femi Gbajabiamila?

Femi Gbajabiamila Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Gbajabiamila ya shafe shekara 16 a majalisar wakilan Najeriya

An zabi Femi Gbajabiamila a karon farko a matsayin dan majalisar tarayya a shekarar 2003 mai wakiltar mazabar Surulere daga jihar Legas da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Ya yi nasara ne a karkashin tutar jam'iyyar AD kafin daga bisani ta rikide zuwa ACN da kuma APC.

Femi, wanda lauya ne, yana da kwarewa a harkar majalisa kasancewar ya dade yana wakiltar mazabarsa a majalisar ta wakilai.

Ya dade yana ana damawa da shi a harkokin siyasa. Kuma dan siyasar ya taba zama magajin garin birnin Atlanta na kasar Amurka.

Ya zama jagoran marasa rinjaye a majalisa ta bakwai wato zamanin shugabancin Aminu Waziri Tambuwal.

Sannan ya zama jagoran masu rinjaye a majalisa ta 8 - wato majalisar da ta gabace wannan sabuwar majalisar ta 9.

An haife shi ne ranar 25 ga watan Yunin shekarar 1962 a jihar Legas.

Ya fara karatun firamare a Mainland Preparatory School da ke jihar Legas yana dan shekara hudu.

Ya kammala digirinsa na farko a kan fannin lauya daga jami'ar Legas a shekarar 1983 bayan ya kammala kwalejin King Williams College da ke Birtaniya.